SHIN A INANE AKE DAURA ANNIYAR YIN SALLAH?



SHIN A INANE AKE DAURA ANNIYAR YIN SALLAH?

*TAMBAYA*❓

Asalamu alaikum warahmatullah. Malam ina tambaya akan niyyar sallah ne. Wato a wane bagirene niyyar sallah take tabbatuwa acikin wadannan wurare; nafarko
1. Lokacin da mutum ya dau abin buta ko shantali zaiyi alwala?
2. Bayan gama alwala kafin a tadda iqama?
3. Bayan tadda iqama kafin kabbarar harama?.

*AMSA*👇

Niyyah abu ce mai muhimmancin gaske saboda ita ce ruhin ayuka kuma saida niyya dukkan ayuka suke tabbata. Saboda fadar Annabi sallallahu alaihi wasallam:

‏( ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺍﻷَﻋْﻤَﺎﻝُ ﺑِﺎﻟﻨِّﻴَّﺎﺕِ ، ﻭَﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻟِﻜُﻞِّ ﺍﻣْﺮِﺉٍ ﻣَﺎ ﻧَﻮَﻯ ‏) ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏(1 ‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 1907 ‏)

Ma'ana: "Lallai dukkan ayyuka suna tare da niyyoyinsu, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya (a zuciyarsa). Bukhari (1) da Muslim (1907) suka ruwaito shi.

Saboda haka shi yasa NIYYAH take sanya ayyukan da yake halal ne su zamo ibadah (wato su zama bautar Ubangiji).

Saboda haka a duk lokacinda mutum ya nasarta yin sallah ko mutum ya tashi ya dauki gora ko butar alwalarsa ya nufi yin tsarki to wannan yayi niyyar yin alwala kenan. Sai kuma a lokacinda mutum yazo ya tsaya zayyi sallah kuma yasan wannan sallar da zayyi sallah kaza ce misali idan Maghrib zayyi yasan cewa Maghrib ce zayyi, ya dauri anniya yin sallar to wannan shima yayi niyyar yin sallar Maghrib ba wai sai ya fada cewa yayi niyyar sallah kaza ba.

Wallahu A'alamu

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)