WACE CE RUMAISA? 8


WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)
  
                             ❓

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

FUTOWA TA 👇
      (8)

KYAUTARTA GA MANZAN ALLAH SAW

  Bukhari ya rawaito daga wajan babban sahabi Anas dan malik yake cewa wata rana manzan Allah (saw) yazo wuce wa ta kusa da gonar ummu Suleim sai ya shiga ciki ya yi mata sallama, sai nace mata manzan Allah (saw) fa ya kasance ya angonce da zainab, sai ummu Suleim tace mai zai hana mukai masa kyauta sai nace mata eh mu'aikata hakan sai ta tashi ta dauko dabino da mai sai ta hada chukuy sai ta turani na kai masa sai yace ajiye, sannan ya umarceni da naje na kirawo masa wasu mutane sai ya ambacesu sannan yace na kirawo masa duk wanda na hadu dashi, sai na aikata abun da ya umarceni sai na dawo ina zuwa naga gidan ya cika maqil da mutane, sai naga manzan Allah (saw) ya saka hannunsa acikin wannan chukuy din sai ya yi abun da ubangiji ya so ya yi aciki sannan sai ya fara kiran mutane goma goma suna ci sai yace dasu ku ambaci sunan Allah kuma kowa yaci abun da ke gabansa. 
  Wannan na nuna mana qaunar ummu Suleim ga manzan Allah (saw) wajan san yi masa kyauta ubangiji ka bamu Albarkacin wadannan bayin Allah ka shiryar da wadanda suke aibatasu ko su zagesu Ameen ya hayyu ya qayyum.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MU HADU A FUTOWA TA 09

Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️
         Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar
             (Abu Rumaisa)
          🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)