WACECE RUMAISA? 9


WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)
  
                             ❓

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

FUTOWA TA 👇
         (9)


NAMAN TABARRAKINTA GA MANZAN ALLAH SAW


  An rawaito daga sumama daga Anas cewa ummu Suleim ta kasance tana shimfidawa manzan Allah (saw) shimfida a gidanta domin ya yi baccin qailula akan wannan shimfidar sai Anas yace idan manzan Allah (saw) ya yi bacci sai na dunga tattara gumunsa da gashinsa sai na hadasu na saka acikin kwalba sannan sai na saka acikin kwano. 
  Sai yace lokacin da Anas yazo gargarar mutuwa sai ya yi min wasiyya akan cewa a saka wanna gumun na manzan Allah (saw) acikin mayafin da za'a yi masa haka kuwa akai bayan mutuwarsa. 
   Haka zalika alokacin da manzan Allah (saw) yaje hajjin bankwana lokacin da mai aski yazo wajansa zai masa aski sai ya raba gashin ban garen damansa ga mutanen da suke bayansa ban garen hagun kuwa ya bawa ita ummu Suleim kadai. 

Ubangiji ka bamu Albarkacin wadannan bayin naka kashiryar da mutanen da suke sukarsu idan Kuma ba masu shiryuwane ubangiji kayi mana maganinsu Ameen.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MU HADU A FUTOWA TA 10

Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️
         Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar
             (Abu Rumaisa)
          🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)