WACE CE RUMAISA? 6 & 7

WACE CE RUMAISA (UMMU SULEIM)
  
                             ❓

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

FUTOWA TA 👇
      (6),(7)
  
                   
ADDU'AR MANZAN ALLAH (SAW) GA DANTA ANAS DA KUMA ABINCIN GIDANTA

  Wata rana manzan Allah (saw) ya shiga gidan ummu suleim kamar yadda bukhari ya rawaito sai ta kawo masa dabino da man shanu sai yace "kumai da man ku cikin kwanansa da dabinonku cikin jakarsa domin ni yau ina azumi". 
    Sai ya tashi zuwa wani ban gare daga cikin gidan ya yi sallar nafila bayan ya gama sai ya yiwa ummu suleim addu'a da kuma iyalan gidanta sai tace ya rasulullahi ina da wata "yar buqata sai yace mece ce sai tace yaranka mai maka hidima wato Anas, manzan Allah bai bar wani Alkhairi na duniya da lahira ba face sai da ya nemawa Anas shi, sai yace acikin addu'ar tashi "ya ubangiji ka azurtashi da dukiya da "yaya ka saka masa Albarka aciki". Da kansa Anas yana cewa na kasance mafi tarin dukiyar mutanan madina. 

Addu'ar manzan Allah (saw) ga abincin gidanta

  Anas bn malik yana cewa kamar yadda bukhari da musulim suka rawaito, Abu dalha yace da matarsa ummu suleim haqiqa najiyo sautin manzan Allah (saw) ya yi rauni sai na fahimci yunwa yake ji shin kina da wani abu a wajanki? Sai tace eh sai ta futo da sha'ir da abun gasa gurasa sai ta gasa masa gurasa, sai ta aikeni da naje na kira farin jakada saw sai na tafi ina zuwa masallaci sai naga manzan Allah saw tare da mutane sai na tsaya akansu sai yace dani Abu dalha ne ya aikoka sai nace eh sai yace da abinci sai nace eh, sai manzan Allah saw ya cewa wadanda suke tare dashi kutashi mutafi sai muka tafi sai na shiga gabansu ina zuwa sai na bawa abu dalha labarin abun da ya faru sai yace ya ke ummu suleim haqiqa manzan Allah saw yazo tare da mutane gashi bamu da abincin da zamu iya ciyar dasu sai tace ubangiji dai shine masani , sai abu dalha ya tafi yaje ya tari manzan Allah da wadanda suke tare dashi, sai manzan Allah saw yace "yake ummu suleim kawo abun da kike tare dashi "sai ta kawo gurasa sai manzan Allah saw ya umarceta da ta hadata da miya bayan ta gama sai manzan Allah saw ya yi addu'a acikin wannan abincin bayan ya gama sai ya cewa Anas kirawo min mutane guda goma sai ya kirasu suka zo suka ci har sai da suka qoshi sannan suka futa, sai yace qara kirawo min goma haka suma har sai da gaba daya mutanan da suke tare dashi suka ci suka qoshi alokacin mutanan su saba'inne ko tama'nin.


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MU HADU A FUTOWA TA 08

Rubutawa... ✍️✍️✍️✍️✍️
         Dalibi mai neman ilimi Nazifi Yakubu Abubakar
             (Abu Rumaisa)
          🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)