ADDU'AR MAGANIN TALAUCI
*اللَّهمَّ إنِّي أسألُكَ مِن فضلِكَ ورحمتِكَ؛ فإنَّهُ لا يملِكُهُا إلّا أنتَ*
Daga Abdullah bin Mas'ud (RA) ya ce: "Wata rana Manzon Allah (SAW) ya yi bãki, sai ya aika zuwa gurin matansa yana neman abincin da zai ba su, sai (aka yi rashin sa'a) ba a samu komai a gurin kowacce daga cikinsu ba. Sai ya ce: "Ya Allah ina rokonka daga falalarka da rahmarka, domin ba wanda yake mallakarsu [falala da Rahma] sai kai. Kwasam, sai aka kawo wa Manzon Allah (SAW) kyautar akuya gashesshiya. Sai ya ce: Wannan daga falalar Allah ne; kuma muna jiran rahmarsa."
عن عبدالله بن مسعود رضي الله عنه قال: "أضافَ النبيُّ ﷺ ضَيفًا، فأرسَلَ إلى أَزْواجِه يَبْتغي عندَهنَّ طعامًا، فلم يجِدْ عندَ واحدةٍ منهنَّ، فقال: اللهم إنِّي أسألُكَ مِن فَضلِكَ ورحمتِكَ، فإنَّه لا يملِكُها إلّا أنتَ. قال: فأُهدِيَ إليه شاةٌ مَصْليَّةٌ. فقال: هذه مِن فَضلِ اللهِ، ونحنُ ننتظِرُ الرحمةَ
أخرجه الطبراني (١٠/٢٢٠) (١٠٣٧٩)، وأبو نعيم في «حلية الأولياء» (٥/٣٦) وصححه الألباني، "السلسلة الصحيحة" (١٥٤٣) و "صحيح الجامع" (١٢٧٨)
Muna neman tsarin Allah daga talauci.
Allah ka yi mana arzuki