ADDU’AR DA ZAKA YI WA AMARYA RANAR FARKO



ADDU’AR DA ZAKA YI WA AMARYA RANAR FARKO

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum warahma tullahi wabara katuhu Allah ya qara malam lpy da qarin Imani malam tambayata anan shine wace addu'ace ango zai yiwa amarya a ranar farko
Muna godiya Allah yasakawa malam da aljanna


*AMSA*👇

DA farko idan zaka shiga dakin amaryarka, zaka shiga ne da alwala. sannan zaka nemi dan wani abinci mai daraja,
misali: kamar kaza ko tsire da sauransu idan kashiga zaka umurceta itama taje tayi alwala sannan kuyi ma Allah godiya abisa cika maku burinku DA yayi kuyi addu’o’in abisa kanku da dukkan al’ummar da suka amsa gayyatar ku suka halarci wajen daurin aurenku daga nan sai ka dafa kanta ko goshinta sannan ka karanta wannan addu’a

ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻰ ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺧَﻴْﺮَﻫَﺎ ﻭَﺧَﻴْﺮَ ﻣَﺎ ﺟَﺒَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦْ ﺷَﺮِّﻫَﺎ ﻭَﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﺟَﺒَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻪ

” ALLAHUMMA INNEE AS’ALUKA KHAIRAHA WA KHAIRA MA JABALTAHA ALAYYA WA A’UZUBIKA MIN SHARRIHA WA SHARRI MA JABALTAHA ALAIYAYA 

Fassara: “Ya Allah ina roqonKa alherinta da alherin da ka hallice ta a kansa, kuma ina neman tsari daga sharrinta da sharrin da Ka hallice ta a kansa. (Abu Dawud da Ibn Majah da Ibn Sinni suka rawaito).

daga nan kuma sai kuci wannan abinda ka shigo dashi ku dan sha wani abu amma ba’a so mutum yaci abu mai nauyi sosai a irin wannan lokacin daga nan kuma sai ku kusanci juna, tare DA gabatar DA yan’wasanni DA juna kafin kufara gabatar DA ibadar aure kuma akwai addu’o’in DA ake karantawa daidai lokaci jima’i

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺟﻨﺒﻨﺎ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ، ﻭﺟﻨﺐ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﺘﻨﺎ
“Allahumma jannibnash shaitan wajannibish -shaytana ma razaktana”

FASSARA: “Ya Allah Ka nesantar da ni daga shaidan kuma Ka nesantar da shaidan daga abin da Ka azurtamu da shi (Na ’ya’ya), (Bukhari da Muslim ne suka fitar da shi daga Abbas).

ANNABI ( S.A.W) yace “idan aka kaddara samun ciki a wannan saduwar to shaidan ba zai iya cutar dashi ba har abada.

Hakazalika, bayan an kammala ibadar aure ma akwai addu’ar da ake gabatarwa. Ga addu’ar:

“Allahumma lataj’al shaidana fiyma razaqtani nasiban.”

FASSARA: “Ya Allah Kada Ka sanya shaidani ya zamo yana da rabo cikin abin da Ka azurtamu.(Bukhari da Muslim).

Rashin karanta wadannan addu’o’in kan sa a haifi yara marasa tarbiyya. Wadannan addu’o’i na kafin da bayan kammala jima’i, ba wai sai a daren angwanci za a yi kawai ba, har da sauran ranakun da ma’aurata suke saduwa.

WALLAHU A'ALAM

Ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yaɗa ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)