_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH ⚖*_
ANNABI DA SAHABBANSA // 011
.
_Tarihi Ya Nuna Irin Qaunar Da Amina Ta Yi Wa Mahaifin Manzon Allah Saw, Sai Dai Bai Jima Tare Da Ita Ba Mai Abin Ya Amshi Abinsa A Madina, Sai Ta Yanke Shawarar Kai Wa Qabarinsa Ziyara, Ta Fita Tare Da Danta Muhammad Saw, Da Mai Yi Mata Hidima Ummu-aiman Da Surukinta Abdulmuttalib, Ta Zauna Can Wata Guda Sannan Ta Juyo, Sai Dai Wani Rashin Lafiya Mai Tsananin Gaske Ya Sha Kanta, Bayannan Kadan Ita Ma Ta Hadu Da Ajalinta A Abwa' Tsakanin Makka Da Madina._
.
_Kakansa, Abdulmuttalib, Ya Dawo Da Shi Makka Ba Uwa Ba Uba, Tausayinsa Da Qaunarsa Suka Dada Samun Matsuguni A Zuciyarsa, Har Ya Kasance Yana Fifita Shi A Kan Sauran 'ya'yansa, Ibn Hisham Yake Cewa: Abdulmuttalib Yakan Sa A Yi Masa Shimfida A Gindin Qa'aba, Duk 'ya'yansa Ba Mai Iya Zama._
.
_To Sai Annabi Saw Da Yake Yaro Ne Qarami Ya Zo Ya Yi Harde-harde A Kai, Sai Baffanninsa Su Yi Qoqarin Dauke Shi, Abdulmuttalib Ya Ce "Ku Bar Shi, Lamarin Yaronnan Babba Ne" Bayan Annabi Saw Ya Hada Shekara 8 Da Wata 2 Da Kwana 10 Allah Ya Yi Wa Kakansa Abdulmuttalib Rasuwa A Garin Makka, Amma Kafin Rasuwarsa Ya Miqa Shi Ga Dayan 'ya'yansa Wato Abutalib, Shi Baffa Ne A Wurin Annabi Saw._
.
_Kasancewar Qaunar Da Abutalib Ya Gada Ta Annabi Saw Daga Mahaifinsa Abdulmuttalib, Sai Ya Ci Gaba Da Girmama Shi, Ya Dora Shi A Kan Kowa, Ya Ba Shi Kariya Ta Masamman, Ya Yi Ta Samun Sabani Da Mutane A Dalilinsa, In Mun Zo Wurin Za Mu Fadada Bayani Da Yardar Allah, Amma Ko A Wannan Lokacin Akwai Abubuwa Da Dama Da Za Su Ba Mutane Mamaki Game Da Annabi Saw._
.
_Wata Rana Mutane Sun Sami Abutalib Suna Yi Masa Kukan Fari, Da Bushewar Qasa Da Buqatar Noma Da Shuka, Abutalib Ya Fita Tare Da Dan-dansa Muhammad Saw, Amma Suna Isa Masallaci Wani Abu Na Ban Mamaki Ya Faru Tare Da Annabi Saw, Yadda Shi Abutalib Ya Ga Fuskar Annabi Saw Tana Haske, Har Dai Zuwa Wani Lokaci Sararin Samaniya Ya Hada Hadari Sai Kuma Ruwa._
.
_Da Annabi Saw Ya Cika Shekara 12 Zuwa 12 Da Wata 2 Da Kwana 10, Abutalib Ya Sumbuce Shi Sai Qasar Sham Don Kasuwanci Kamar Yadda Suka Saba, Har Dai Ya Kai Basra, A Lokacin Ana Sanya Ta A Qasar Sham Ne Ba Iraq Ba, To Qasba Tana Qarqashin Mulkin Rum Ne Kamar Yadda Muka Yi Bayani A Baya, A Nan Ne Suka Yi Arba Da Pastor Wanda Aka San Shi Da Buhaira, Amma Sunansa Na Sosai Jarjis, Lokacin Da Ayarin Suka Isa Ya Fito Ya Yi Musu Barka Da Isowa Ya Karrama Su._
.
_Abin Al'ajabi A Ciki Shi Ne Wannan Pastor Din A Baya Bai Zuwa Wurin Ayari, Sai Wannan Karon, Yana Zuwa Kuma Ya Fahimci Annabi Saw Sabo Da Sufofinsa Da Suka Bayyana, Sai Ya Kama Hannunsa Yana Cewa: "Wannan Shi Ne Shugaban Al'umma, Shi Ne Wanda Allah Zai Aiko Don Ya Zama Rahama Gare Su" Sai Abutalib Ya Ce "Ta Ya Ka San Haka?"_
.
_Pastor Din Ya Ce: " Lokacin Da Kuka Hawo Yankin Aqaba Duk Wani Dutse Sunkuyawa Yake Yi Don Sujada, Su Kuwa Ba Mahalukin Da Suke Yi Wa Sujada In Ba Annabi Ba, Sannan Akwai Alamar Annabta Kamar Tuffah A Qasan Kafadarsa, Wannan Yana Rubuce A Littafammu, Daganan Ne Ya Roqi Abutalib Da Ya Mai Da Shi Gida Kar Ya Qarisa Da Shi Cikin Sham Sabo Da Tsoron Yahudawa, Sai Abutalib Ya Hada Shi Da Wasu Yara Ya Ce Su Raka Shi Makka._
.
_Lokacin Da Annabi Saw Ya Kai Shekara 15 Ne Aka Yi Yaqin Fujjar, Yaqi Ne Tsakanin Quraishawa Da Qawayensu Da Kuma Qais Ilan, A Lokacin Harb Bn Umayya Shi Ne Kwamandan Qwaraish Da Kinana Gaba Daya, Sabo Da Girmansa Da Matsayinsa, Da Sanyin Safiya Dai Qais Ne Suka Rinjayi Kinana, Amma Da Rana Ta Yi Sai Yaqi Ya Juya, Kinana Suka Hau Kan Qais, An Kira Yaqin Na Fujjar Sabo Da An Yi Shi A Watannin Alfarma, Annabi Saw Ya Halarci Yaqin, Ya Riqa Shirya Musu Kibau._
_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
