CUTUTTUKAN ZAMANIN DAN ADAM.



CUTUTTUKAN ZAMANIN DAN ADAM.
-
"Wato dukkanin wata kariya da kake samu a rayuwarka, bawai wayonka bane yake baka ita, a'a. Lallai wannan wata rahama ce daga buwayayyen sarki wanda shi ke da iko a kan komai"
-
"Cuta tazo ta tafi, wata ta sameka wata kuma ta wuce ka, lallai babu mai ƙaddara hakan sai Allah, kullum mukan kasance cikin tararrazi na rashin sanin afkuwar wata cuta a garemu, domin muna ganin yadda take yin tasiri a kan waɗansu waɗanda ba mu ba, mu kuma Allah sai ya karemu daga gareta"
-
"Allah buwayi ya saukar da cututtuka masu tarin yawa a rayuwar ɗan adam, wasu mun sansu sosai sabida yawan kai-kawonsu a cikinmu, wasu kuma sunansu kawai muke ji amma bamu taɓa kamuwa dasu ba, kuma bamu taɓa ganin wanda ya kamu dasu ba, wasu kuma bamu taɓa kamuwa dasu ba amma kuma munga waɗanda suka taɓa kamuwa dasu, wannan haka sunnar Allah take, inda yaso sai kaga ya saukar maka da cutar da baka taɓa jin ta bama a tarihin rayuwarka, amma sabida jin-ƙai da tausayinsa gareka, sai ya kareka daga gareta, Yaa Allah mun daɗa gode maka"
-
Biyo Instagram É—inmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
Facebook group
https://www.facebook.com/groups/4329860357034439/?ref=share
Post a Comment (0)