HAƘURI A GIDAN MIJI ZAI GADAR MAKI DA KARSHE MAI KYAU GAMI DA NASARA DUNIYA DA LAHIRA

👌🏼 HAƘURI A GIDAN MIJI ZAI GADAR MAKI DA KARSHE MAI KYAU GAMI DA NASARA DUNIYA DA LAHIRA 👌🏼



🌴 Shaykh Uthaimeen Allah ya masa rahama yana cewa; "Idan har mata tayi hakuri ta nemi lada a wurin Ubangijinta sannan tayi dakon mafita daga wurin Allah, ta kuma sauke hakkin mijinta da Allah ya dora mata koda kuwa shi mijin ya tauye mata nata hakkin, to lallai nasara da kyakkyawan karshe na gareta. Wanda kuma wannan itace qa'ida ga duk wanda yake da hakki akanka, idan har kai ka sauke naka hakkin shi kuma yaki saukewa to sai Allah ya doraka akansa".

🌴 Ya cigaba da cewa: "Dalili kuwa hadisin Manzon Allah, wanda sahabi Abi huraira ya ruwaito* yace _"Wani mutumi yazo wurin Manzon Allah_ yace: "Ya manzon Allah na kasance ina da yan uwa wadanda ina sadar masu da zumunci amma su suna yanke min, ina kyautata masu, amma su suna munanta min, ina hakuri dasu amma su suna min jafa'i." Sai Manzon Allah yace masa "Idan har ka kasance kamar yadda ka fada to kana nan kamar kana ciyar dasu tokace Mai zafi, kuma ba zaka gushe ba Allah yana baka kariya da taimako ba har abada matukar kana nan a haka baka sauya ba"
📒 مسلم ٢٥٥٨ . 

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)