MAZA KA/KI TUBA GA ALLAH



☆★☆MAZA KA/KI TUBA GA ALLAH☆★☆

lallai yawan sabon Allah da zunubai na nesanta mutum daga rahamar Allah, zuciya tayi baqin qirin, ta rasa walwala, jin dadi, natsuwa da kwanciyan hankali, sai qunci da damuwa da tabarbarewan lamurra su maye gurbi.

Babu alkhairi ga mutanen da suke dogewa akan sabo. yawaita tuba da istigfaari abune mai matuqar mahimmanci.

Allah yana farin ciki da bawan da yayi laifi kuma ya tuba ya dawo gareshi.

Allah yace:-

"ومن يعمل سوءا أو يظلم نفسه ثم يستغفر الله يجد الله غفورا رحيما" (النساء 110)

"Kuma wanda ya aikata mummuna ko ya zalumci kansa sa'annan ya nemi gafarar Allah, zai sami Allah mai gafara mai jinkai"

Kuma yace:-

"والذين إذا فعلوا فاحشة أو ظلموا أنفسهم ذكروا الله فاستغفروا لذنوبهم ومن يغفروا الذنوب إلا الله ولم يصروا على ما فعلوا وهم يعلمون"

"Kuma wadanda idan suka aikata wani alfasha ko suka zalumci kansu sai su tuna Allah, sai su nemi gafarar zunubansu. Kuma wake gafarar zunubai face Allah? Kuma basu doge akan abinda suka aikata ba alhali kuma suna sane."

Ya kuma ce:-

"قل يا عبادي الذين أسرفوا على أنفسهم لا تقنطوا من رحمة الله، إن الله يغفر الذنوب جميعا، إنه هو الغفور الرحيم". (53)

وأنيبوا إلى ربكم وأسلموا له من قبل أن يأتيكم العذاب ثم لا تنصرون". (54)

واتبعوا أحسن ما أنزل إليكم من ربكم من قبل أن يأتيكم العذاب بغتة وأنتم لا تشعرون(55)"

"Kace ya bayina wanda sukayi barna akan kawunansu, kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah. Lallai Allah na gafarta zunubai baki daya, lallai Shine mai gafara mai jin kai." (53)

"Kuma ku mayar da al'amuranku ga Ubangijinku, kuma ku sallama masa, kafin azaba tazo muku wannan lokacin bazaa taimakeku ba."(54)

"Kuma ku bi mafi kyawun abinda aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kafin azaba tazo muku ba tsammani kuma ku baku sani ba".(55)

☆Mu zama masu tuba daga zunubanmu tun kafin lokaci ya qure mana inda nadama bazatayi amfani ba!

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24
Post a Comment (0)