Ina So Na Haɗu Da Mijina Na Farko A Aljanna, Ko Zai Yiwu?
*TAMBAYA*❓
Malam matar da mijinta ya mutu, sai tayi wani auren shin zata sake haɗuwa da na farkon a lahira, in dukansu sun shiga Aljanna, ko kuma na karshen shine zai zama mijinta a can ?
*AMSA*👇
To yar’uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas’alar zuwa zantuttuka uku:
1. Za ta zauna da wanda yafi kyawawan dabi’u a duniya
2. Za’a ba ta zabi.
3. Zata zauna da na karshensu, Wannan maganar ita ce mafi inganci, Saboda fadin Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi cewa: “Duk matar da mijinta ya mutu, tayi aure a bayansa, to ranar lahira zata kasance ga na karshensu” Albani ya inganta shi a Sahihu-jamiussagir hadisi mai lamba ta : 2704, Wannan kuma shi ne dalilin da ya hana matar Abuddarda’a aure bayan mijinta ya mutu, lokacin da Mu’awiya ya nemi ya aure ta, taki yarda ta aure shi, saboda tana so ta zauna da Abudarda’a a lahira. A duba silsilasahiha hadisi mai lamba ta: 1281. Munawy yana cewa: “Malamai suna cewa: Wannan shine daya daga cikin dalilan da suka sa matayan Annabi (s.a.w) ba suyi aure ba bayansa, saboda Allah ya riga ya kaddara cewa: matayansa ne a Aljanna” duba Faidhul- kadeer 3\151
Allah ne mafi sani.
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177