•┈┈••🍃••┈┈•
KU YI BUSHARA YA KU MA'ABOTA HAƘURI
Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:
"إِنَّمَا يُوَفَّى الصَّابِرُونَ أَجْرَهُم بِغَيْرِ حِسَابٍ".
{الزمر :10}
"Mãsu haƙuri kadai a ke cika wa sakamakonsu, bã da wani lissãfi ba".
Wannan kuwa ya ƙunshi dukkan haƙuri:
●Haƙuri a kan ƙaddarorin Allah kar da bawa yayi fushi ko ya ƙi yarda da ƙaddara.
●Haƙuri a kan saɓon Allah, kar da ya aikata.
●Haƙuri a kan ɗa'a ga Allah, yayi biyayya da aiwatar da ita.
Sai Allah ya yi alƙawarin sakamako ga masu haƙuri ba tare da ƙididdigewa ba: Ma'ana ba tare da haddi ko iyakancewa ba, wannan kuma saboda falala da matsayin haƙuri ne a gurin Allah, kuma shine mai taimako a kan dukkan lamurra.
تفسير السعدي
# Zaurandalibanilimi
TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi
INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24