KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 07



KAFOFIN SADA ZUMUNTA NA ZAMANI A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI // 07
.
Mawallafi: Sheikh Aliyu Said Gamawa
.
Saƙo tsakanin Annabi Sulaiman (A.S) da tsunstu alhuda-huda da kuma Ifritu daga jinsin aljanu³.
وورث سليمان داوود وقال يأيها الناس علمنا منطق الطير وأوتينا من كل شيء إن هذا لهو الفضل المبين (١٦) وحشر لسليمان جنوده من الجن والإنس والطير فهم يوزعون (١٧) حتى إذا أتوا على واد النمل قالت نملة يأيها النمل ادخلوا مسكنكم لا يحطمنكم سليمان وجنوده وهم لا يشعرون (١٨) فتبسم ضاحكا من قولها وقال رب أوزعني أن أشكر نعمتك التي أنعمت علي وعلى والدي وأن أعمل صالحا ترضاه وأدخلني برحمتك في عبادك الصالحين (١٩).
.
"Kuma Sulaiman ya gaji Dawuda ya ce, 'Ya ku mutane! An sanar da mu maganar tsuntsaye, kuma an ba mu daga kowane abu, lalle ne wannan, haƙiƙa shi ne falalar (Allah) bayyananna". "Kuma aka tattara domin Sulaiman, rundunoninsa daga aljanu da mutane da tsuntsaye, to su ana kange su (ga tafiya)". "Har a lokacin da suka je rafin tururuwa, wata tururuwa ta ce 'Ya ku jama'ar tururuawa! Ku shiga gidajenku kada Sulaiman da rundunoninsa su kakkarya ku, alhali ba su sani ba".
.
"Sai ya yi murmushi yana mai dariya daga maganarta, kuma ya ce 'Ya Ubangijina! Ka cusa mini in gode wa ni'imarka wadda ka ni'imta ta a gare ni, da kuma mahaifana biyu, kuma in aikata aiki na ƙwarai, wanda kake yarda da shi, kuma ka shigar da ni, saboda rahmarka a cikin bayinka salihai...".
.
Sannan akwai sadarwa tsakanin Ubangiji (S.W.T) da Annabi Musa (A.S) a Duri-sina⁴.
وجاوزنا ببني إسرائيل البحر فأتوا على قوم يعكفون على أصنامهم قالوا يا موسى اجعل لنا إلها كمالهم آلهة قال إنكم قوم تجهلون (١٣٨) إن هؤلاء متبر ما هم فيه وباطل ما كانوا يعملون (١٣٩) قال أغير الله أبغيكم إلها وهو فضلكم على العلمين (١٤٠) وإذ أنجيناكم من آل فرعون يسومون كم سوء العذاب يقتلون أبناءكم ويستحيون نساءكم وفي ذلكم بلاء من ربكم عظيم (١٤١).
.
"Kuma muka ƙetarar da bani Isra'ila ga teku, sai suka je a kan wasu mutane waɗanda suna lizimta da ibada a kan wasu gumaka nasu, suka ce 'Ya Musa! Ka sanya mana wani abin bautawa kamar yadda suke da abin bautawa". "Ya ce 'Lalle ku, mutane ne kuna jahilta". "Lalle waɗannan, abin da suke bauta wa halakakke ne, kuma abin da suka kasance suna aikatawa ƙarya ne".
.
"Ya ce 'Shin wanin Allah nake nema muku ya zama abin bautawa alhali kuwa shi (Allah) ya fifita ku a kan halittu?". "Kuma a lokacin da muka tsirar da ku daga mutanen Fir'auna suna taya muku mugunyar azaba, suna karkashe ɗiyanku maza, kuma suna rayar da matanku, kuma a cikin wannan akwai jarrabawa daga Ubangijinku mai girma...".
.
ولقد آتينا موسى تسع آيات بينات فاسأل بني إسرائيل إذجاءهم فقال له فرعون إني لأظنك يا موسى مسحورا (١٠١) قال لقد علمت ما أنزل هؤلاء إلا رب السموت والأرض بصائر وإني لأظنك يا فرعون مثبورا (١٠٢).
"Kuma lalle ne, haƙiƙa mun bai wa Musa ayoyi guda tara bayyanannu, sai ka tambayi bani Isra'ila, a lokacin da ya je musu, sai Fir'auna ya ce masa lalle ni ina zaton ka Ya Musa sihirtacce". "Ya ce 'Lalle ne, haƙiƙa ka sani babu wanda ya saukar da waɗannan face Ubangijin sammai da ƙasa, don su zama abubuwan lura, kuma lalle ne ni, haƙiƙa ina zaton ka ya Fir'auna halakakke".
.
إذ قال موسى لأهله إني آنست نارا سآتيكم منها بخبر أو آتيكم بشهاب قبس لعلكم تصطلون (٧) فلما جاءها نودي أن بورك من في النار ومن حولها وسبحان الله رب العالمين (٨)
"A lokacin da Musa ya ce wa iyalinsa, 'Lalle ni na tsinkayi wata wuta, ni mai zo muku daga gare ta ne, da wani labari ko kuwa mai zo muku ne da yula, makamashin, tsammaninku ku ji ɗumi". "To lokacin da ya je mata, sai aka kira shi cewa, An tsarkake wanda yake cikin (wurin) wutar da wamda yake a gefenta, kuma tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin halittu".
.
Sai kuma saƙo na Isra'i da Mi'iraji tsakaninsa da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W)5.
سبحان الذي أسرى بعبده ليلا من المسجد الحرام إلى المسجد الأقصى الذي باركنا حوله لنريه من آياتنا إنه هو السميع العليم (١). (سورة الإسراء، آية ١).
"Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawansa da dare daga masallaci mai alfarma zuwa ga masallaci mai nisa, wanda muka sanya albarka a gefensa domin mu nuna masa daga ayoyinmu, lalle ne shi, shi ne mai ji, mai gani".
.
Irin waɗannan nau'uka na saƙonni wadda aka same su ta hanyar wahayi ko nassi, su ne kowane musulmi ke iya bugan ƙirji ya isar da su ba tare da wata tababa ba, domin dukkanin su tabbas ne, babu abin kokwanto a cikinsu.
_________
³Suratu 27: 16-20.
⁴Sura 7: 138-141, 17: 101-102, 27: 7-8.
5 Sura 17: 1.


.

Rubutawa:- Shaikh Aliyu sa'id Gamawa
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)