KARANTA KA QARU (03)



KARANTA KA QARU (03)
**********************
🔘 Mahaifiyar Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib, wato Sayyidah Fatimah bintu Asad, ita ce farkon mace Bahashimiya wacce ta haifi 'ya'ya Hashimawa. 

🔘 Mahaifinta Asadu 'dan uwan Abdul Muttalibi ne, kuma dukkansu 'ya'yan Hashim ne. 

🔘 Wato da ita da mahaifin Annabi ﷺ 'ya'yan Baffanu ne kenan. Ta daya bangaren kuma, da Mijinta Abu Talib da Abdullahi mahaifin Manzon Allah ﷺ Shaqiqai ne. (mahaifi da mahaifiyarsu guda).

🔘 Ta musulunta har ma tayi hijira zuwa Madeenah, kuma achan ta rasu. Kuma yayin da akazo binneta sai da Manzon Allah ï·º ya shiga cikin Qabarin ya kwanta sannan ya fito yayi mata addu'a. 

🔘 Kuma ita ce farkon Bahsshimiyar da ta haifi Khalifah daga cikin Khalifofin Musulunci. Wato Shugabanmu Aliyu 'dan Abu Talib (Karramal Lahu Wajhahu).

🔘 Bayan ita sai kuma Nana Fatimah 'Yar Annabi Muhammadu ï·º itama ta haifi Khalifah. Shine Shugabanmu Alhasan 'dan Aliyu 'dan Abu Talib (Allah ya yarda dasu) yayi khalifanci tsawon watanni shida bayan an shahadantar da mahaifinsa (aminci da yardar Allah ta tabbata gareshi da dukkan iyalan gidan Manzanci baki 'dayansu). 

🔘 Ta ukunsu ita ce Zubaidah matar Khalifah Harunur Rasheed ta haifa masa 'dansa Al-Ameen wanda shima ya rike Khalifancin daular Musulunci ta banul Abbas kafin 'dan uwansa Ma'amun ya tub'eshi ya kasheshi.

🔘 Mahaifiyar Sayyiduna Hamzah (ra) sunanta Haalah bintu Wuhaib bn Abdi Manaf bn Zuhrata. 

🔘 Da mahaifiyar Sayyiduna Hamza da Mahaifiyar Manzon Allah ï·º kakansu 'daya. Wato 'ya'yan baffanu ne. Ita Shugabarmu Aminatu 'yar Wahbu ce, ita kuma Haalah 'yar Wuhaibu ce. Da Wahbu da Wuhaibu din Wa da Qani ne. 

🔘 Bayan wannan kuma, Sayyiduna Hamzah ya ha'du da Annabin Rahama ï·º ta bangaren shayarwa. Suwaibatul Aslamiyyah ta shayar dasu duk su biyun, Sannan kuma matar da ta shayar da Sayyiduna Hamza acikin Qabilar Banu Sa'ad ta ta'ba karbar Manzon Allah ï·º daga hannun Halimatus Sa'adiyyah ta shayar dashi tsawon wuni guda. 

🔘 Bisa wannan dalilin ne lokacin da Sayyiduna Aliyu ya kawo wa Manzon Allah ﷺ shawarar ko zai auri 'yar gidan Sayyiduna Hamzah?

Sai yace masa "A'a ai 'yar 'dan uwan shayarwata ne. Suwaibah ta shayar dani da Hamzah (riwayar Bukhariy da Muslim). 

Nan zan tsaya, ina fatan mai karatu ya Qaru da abinda ya karanta. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (01/01/2022 27/05/1443)

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)