MACEN DA BA A IYA SAKI 12

MACEN DA BA'A IYA SAKI............




🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(12)*

*KIYI HAQURI AKAN TALAUCIN MIJINKI*

    Ya "yar uwa mai daraja ki sani cewa talauci ba aibi bane, rashin haquri akan sa shi ne aibi, da kuma rashin tashi haiqan wajan korar sa daga cikin gida. 
     Ya "yar uwa mai Albarka ki sani ba'a taba yin wani mutum ada ko yanzu ko nan gaba da Allah subhanahu wata'ala yake kaunar sa sama da farin jakada babba dan Abdullah Muhammadurrasulullah saw amma ummuna Aisha Allah ya qara mata yarda take cewa "Iyalan manzan Allah saw basu taba koshi da gurasa ta sha'ir kwanaki biyu ajere ba har ubangiji ya karbi rayuwar sa". 
   Ta qara da cewa ya kai dan "yar uwa ta mun Kasan ce muna ganin jinjirin wata sannan mu kara gani sannan mu kara gani jira jiran wata guda uku cikin wata biyu, ba'a kunne wutar murhu acikin gidan manzan Allah saw ba, sai urwa yace ya ke goggo dame kuke rayuwa? Sai tace masa ba kake guda biyu dabino da ruwa. 
    Haka zalika matan magaba ta na kwarai suke haquri da talaucin mazajen su, wani mutum a garin madina ya kasance da zarar manzan Allah saw ya yi sallama daga sallah sai yai sauri ya futa daga masallaci, wata rana sai manzan Allah saw ya tsayar dashi yake tambayar sa dalilin da yasa yake wannan saurin, sai yace ya manzan Allah saw ni da mata ta bamu da tufafi face wannan tufafin idan nayi sallah dashi sai nayi sauri naje gida na bata itama ta saka tayi sallah. 
   Ya yin da wannan mutumin ya bar wajan manzan Allah saw ya koma gida sai matar tasa take tambayar sa dalilin da yasa yai jin kirin dawo wa daga masallaci sai ya gaya mata yadda sukai da manzan Allah saw, budar bakin ta sai tace ya kai bawan Allah yanzu karar Allah ka kai wajan manzan sa saw?. 
   Daga lokacin tace aurena dakai ya kare Allahu Akhbar,,, ya "yar uwa mai daraja kalli yadda haqurin wannan baiwar Allah yake duk da cewa mai gidan nata baiyi wani laifi ba, amma kalli amsar da ta bawa mijin nata. 
    Ya "yar uwa mai Albarka kiyi haquri da halin da mijinki ya tsinci kansa aciki, baki san nan gaba ya zai zama ba, kuma ki dunga duba zuwa ga wasu wadanda basu kai ki ba hakan zai sa ki godewa ni'imar Ubangijin al'arshi gare ki, tabbas idan kika siffantu da wannan siffar kece macen da nake wa laqabi da macen da ba'a iya saka.
   

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 13*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)