MACEN DA BA A IYA SAKI 13

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(13)*



   *KI KULA DA BAQIN MIJINKI*

    Ya "yar uwa mai daraja ki sani cewa babu wani bako da zai ziyarci gidanki face yazo da arziqinsa kuma ya tafiyar muku da zunubanku, don haka baqin mijin ki su zama baqin ki, kula wa da su martaba su, girmama mijin ki ne, haka zalika wulaqan ta su, wulaqanta mijin ki ne. 
   Farin jakada babban dan Abdullah Muhammadurrasulullah saw yana cewa "Duk wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira ya girmama baqon sa". 
    Wata rana wani mutum yazo wajan manzan Allah saw sai yace ya manzan Allah ina cikin matsananciyar yunwa sai manzan Allah saw ya aika zuwa wajan mata yensa duk kanin su ko wacce tace masa na rantse da wanda ya aikoka da gaskiya babu komai a waje na sai ruwa, sai manzan Allah saw ya cewa sahabbai shin acikinku wa zai bakuntar da wannan bakon sai wani mutum daga cikin mutanen madina yace nine ya manzan Allah, bayan zuwan sa gida sai ya cewa matar sa, shin akwai wani abu a wajan ki sai tace a a sai dai abincin yaran mu, sai yace ki sa suyi bacci da wani abun, bayan bakon mu ya shigo ki mike zuwa wajan futula ki kashe ta, mu nuna masa kamar muna ci, haka akai bakon nan yacin ye abincin, da gari ya waye wannan mutumin yazo wajan manzan Allah saw sai yace masa haqiqa Ubangiji ya yi mamaki da abun da kukayi kai da matar ka, sai Ubangiji ya saukar da aya akan wadannan bayin nasa. 
    Ya "yar uwa mai daraja kalli wannan baiwar abun da ta aikata domin ta futar da mijin ta daga cikin kunya, shin wannan bawan Allah zai iya rabuwa da wannan matar kuwa? 
   Don haka "yar uwa mai Albarka ki bada kulawa ta musamman ga bakin Mijin ki kamar yadda zaki kula da naki hakan zai janyo miki abubuwa guda biyu daya lada wajan mahaliccin ki, daya kuma samun qauna ta musamman daga wajan mai gidanki tabbas idan kina karrama bakin mijin ki da girmama su kece macen da na kewa laqabi da macen da ba'a iya saka.
   

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 14*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)