MACEN DA BA A IYA SAKI 15

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(14)*


*NISANTAR TAURIN KAI DA SAN ZUCIYA*

    Ya "yar uwata mai daraja ki sani cewa taurin kai gaba ki dayan sa sharri ne, haka zalika bin san zuciya yana jawo kunci cikin rayuwar auratayyar, don haka "yar uwa yi kokari wajan nisantar su domin musibune. 
     Masu hikima suna cewa taurin kai da san zuciya wuta ce duk lokacin da ta kunnu acikin gida sai ta kona gidan baki daya. 
    Haka zalika wata mahaifiya tana yiwa "yarta nasiha kafin auren ta, take cewa " Ya ke "yata ina gargadarki da taurin kai, domin yana korar miji daga cikin gida kamar yadda hayaqi yake korar zuma". 
    Haka zalika wata mata tana bada labarin taurin kai da taiwa mijinta da kuma yadda take bin san zuciyarta take cewa : Na auri wani mutum ya kasance yana matuqar qaunata, ni kuma na Kasance ina masa taurin kai ina saba masa har sai da ya gaji dani ya kyamace ni, amma bai sake ni ba, sai ya auri wata mata mai kyakykyawar dabi'a kuma ya samu jin dadi da hutu a wajan ta, mai makon na rage abun da nake sai na kara taurin kai na, sai ya sake ni, sai naje na auri wani mutum wanda bai kai mijina na baya ba ta ko ina mijina na baya ya fi sa, ina masa komai amma shi kuma baya bani komai, yana yawan zagina da bakaken maganganu, daga nan sai na fahimci cewa sakayya ce ubangiji yake min akan abun da na aikata na butulcewa ni'imar da ya yimin ta mijina na farko". 
     Ya "yar uwata mai daraja ki sani taurin kai da bin san zuciya wasu miyagun dabi'u ne da zasu kaiki zuwa nadama, duk lokacin da kike masa taurin kai hakan zai kai zuwa ga rasa soyayyar ki a wajan sa domin ita zuciya an ginata akan san wanda yake kyauta ta mata da kuma kin wanda yake munana mata, dole sai sanki ya fuce daga cikin zuciyar sa, akarshe mai faruwa sai ta faru shine saki, amma duk lokacin da kika nisanci wadannan miyagun dabi'un kece nake wa laqabi da macen da ba'a iya saka.
    
*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 15*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)