SHIN A INANE AKE DAURA ANNIYAR YIN SALLAH, SANNAN KUMA SHIN YA HALASTA MATA SUYI KASUWANCI??

SHIN A INANE AKE DAURA ANNIYAR YIN SALLAH, SANNAN KUMA SHIN YA HALASTA MATA SUYI KASUWANCI??

Asalamu alaikum warahmatullah. Malam ina tambaya akan niyyar sallah ne. Wato a wane bagirene niyyar sallah take tabbatuwa acikin wadannan wurare; nafarko
1. Lokacin da mutum ya dau abin buta ko shantali zaiyi alwala?
Na biyu
2. Bayan gama alwala kafin a tadda iqama?
Na uku
3. Bayan tadda iqama kafin kabbarar harama?.
Tambaya ta biyu shin ko ya halasta mata suyi kasuwanci a muslunci?

AMSA:

الحمدلله

Niyyah abu ce mai muhimmancin gaske saboda ita ce ruhin ayuka kuma saida niyya dukkan ayuka suke tabbata. Saboda fadar Annabi sallallahu alaihi wasallam:

‏( ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺍﻷَﻋْﻤَﺎﻝُ ﺑِﺎﻟﻨِّﻴَّﺎﺕِ ، ﻭَﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻟِﻜُﻞِّ ﺍﻣْﺮِﺉٍ ﻣَﺎ ﻧَﻮَﻯ ‏) ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏(1 ‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 1907 ‏)

Ma'ana: "Lallai dukkan ayyuka suna tare da niyyoyinsu, kuma lallai kowane mutum yana samun sakamakon abinda yayi niyya (a zuciyarsa). Bukhari (1) da Muslim (1907) suka ruwaito shi.

Saboda haka shi yasa NIYYAH take sanya ayyukan da yake halal ne su zamo ibadah (wato su zama bautar Ubangiji).

Saboda haka a duk lokacinda mutum ya nasarta yin sallah ko  mutum ya tashi ya dauki gora ko butar alwalarsa ya nufi yin tsarki to wannan yayi niyyar yin alwala kenan. Sai kuma a lokacinda mutum yazo ya tsaya zayyi sallah kuma yasan wannan sallar da zayyi sallah kaza ce misali idan Maghrib zayyi yasan cewa Maghrib ce zayyi, ya dauri anniya yin sallar to wannan shima yayi niyyar yin sallar Maghrib ba wai sai ya fada cewa yayi niyyar sallah kaza ba.

2. Tambayarka ta biyu:

Eh halatta mata su yi kasuwanci a cikin gidajensu ko kuma a waje muddin zasu kiyaye abinda shari'ah ta tanada wato kada su nuna tsiraicinsu, kada suyi tafiya ba tare da muharraminsu ba, kada su rinka nuna kwalliyarsu wato su saka hijab, kada suyi cudanya da maza, kada su rinka kashewa abokan kasuwanci maza murya yayin cinikayya, a takaice dai su kiyaye da dukkan wata kofa ta fitinah da kuma sabawa Allah da ManzonSa. Dalili kuwa shine fadar Allah subhanahu wata'ala cewa:  "Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba"

‏( ﻭَﺃَﺣَﻞَّ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﺒَﻴْﻊَ ﻭَﺣَﺮَّﻡَ ﺍﻟﺮِّﺑﺎ ‏)

[al-Baqarah 2:275]

Da kuma fadar Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam da aka tambaye shi wane samu ne yafi? Sai yace:

( ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺑﻴﺪﻩ ، ﻭﻛﻞ ﺑﻴﻊ ﻣﺒﺮﻭﺭ ‏)

Wato samun da mutum ya nema da hannuwansa, kuma dukkan huldayyar kasuwanci (wato na halal) mai albarka ne.

Wadannan hukunce-hukuncen sun shafi dukkan musulmi maza da mata.

Haka kuma an ruwaito cewa matan Musulmi na farko suma suna kasuwanci ba tare da nuna tsiraicinsu ba, nuna kwalliyarsu ba, tare da kiyaye dukkan sauran abubuwan dake iya haifar da fitinah da sabon Allah. Amma idan mace tana kasuwanci tana bayyana kwalliyarta da yawace-yawace ba tare da muharrami ba ko kuma cudanya da mazan da ba muharramanta ba to wannan kam haramun ne..

والله أعلم،

***********************************

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

Tambayoyin Musulunci
            WhatsAppGroup

Post a Comment (0)