ZAN IYA DAUKAR AZUMIN NAFILA A JAJIBARIN RAMADAN?

*_ZAN IYA DAUKAN AZUMIN NAFILA A JAJIBARIN RAMADAN?_*

                               *Tambaya*
Assalamu alaikum, Menene hukuncin wanda keyin azumin litinin da alhamis sai azumin Ramadan ya kama ranan juma'ah to ya halasta yayi azumin ranan alhamis din Alhalin washe Gari azumin Ramadan?

                                   *Amsa*
Wa'alaikum assalam, In ya saba yi babu laifi ya azumta, saboda hadisin da Annabi S.A.W yake cewa: " Kada ku gabaci Ramdhana da azumin yini daya ko biyu sai Fa in azumin da mutum ya saba yi ne, kamar yadda Bukhari ya rawaito hakan a hadisi mai lamba ta: 1914 da kuma Muslim a hadisi mai lamba: 1082.

Allah ne mafi sani

17/05/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren MIFTAHUL ILMI (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)