INA SON BIN UMANIN ALLAAH, AMMA ZUCIYA TA TANA SANI SABON ALLAAH, MENENE MAFITA

INA SON BIN UMARNIN ALLAH, AMMA ZUCIYATA TANA SANI SABON ALLAH, MINENE MAFITA? BISMILLAH.

Tambaya?
Salam, malam a cikin zuciyata ina jin tsoron Allah, kuma ina son bin umarnin Allah, saidai ina yawan sabon Allah kuma, malam inaso a taimake ni da shawara akan hakan?

Amsa:
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN QAI.
To dan uwa, ina fatan zaka karanta wannan ‘kissar da idon basira, domin zaka sami shawarar‎ da kake bukata gata kamar haka:

Wata rana wani saurayi yaje wajen Ibrahim ‘dan Adhama, (‘daya daga cikin magabata), sai yace masa zuciyata tana tunkuda ni zuwa sa’bo, kayi min wa’azi. Sai yace masa: “Idan ta kirawo ka zuwa sa’bawa Allah to ka saba masa, amma da sharuda guda biyar. Sai saurayin yace fadi mujisu.

Sai yace:
1. Idan zaka sabawa Allah, to kabuya a wurin da bazai ganka ba, sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah, yaya za’ayi na boye masa, alhalin babu abin da yake ‘buya gareshi?
Sai yace: Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kuma yana ganinka.

2. Idan zaka sabawa Allah to karka saba masa a cikin kasarsa, sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah, ina zanje, alhali duka duniya tasace?
Sai yace masa: Yanzu bakajin kunya kasa’ba masa alhali kana zaune a saman kasarsa?

3. Idan zaka sabawa Allah to kadaina cin arzikinsa. Sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah, ta yaya zan rayu alhali duka ni’imomi daga gareshi suke?
Sai yace masa: Yanzu ba kajin kunya ka sa’ba masa alhali yana ciyar da kai kuma Yana shayar dakai, Yana baka karfi?

4. Idan ka sabawa Allah, to idan mala’iku sukazo tafiya dakai Wuta, kace bazaka tafi ba Aljanna zaka.‎ Sai saurayin yace: Tsarki ya tabbata ga Allah ai sunfi 'karfina, korani zasuyi.

5. Idan ka karanta zunubanka a takardarka ranar alkiyama kace ba kaine ka aikata suba. Sai saurayin yace:‎ Tsarki ya tabbata ga Allah, ina mala'iku masu kiyayewa, sai yafashe da kuka yatafi yana maimaita wannan Kalmar ta karshe.

IN HAR KANA TUNA ‘DAYA DAGA CIKIN WADANNAN IDAN ZAKA AIKATA ZUNUBI, TO TABBAS ZAKAJI KUNYAR ALLAH.

Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki.
Ya Allah ka tsarkake mana zukatanmu daga sabo.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Asuba tagari!

Post a Comment (0)