Ƴar Bautar Ƙasa 20

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*



Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*20*


Tunda suka ɗau hanya bawanda yacewa ɗan uwansa ƙala,se najeeb daya kifa kanshi akan cinya yanata kuka.

"Dallah malam kacikamin kunne da kuka,ubanwa ya sa ka aykata abinda ka aykata,wlh ko yanzu salma ta mutu kaine ka kasheta,wawa kawai wanda besan abinda yake ba"cewar kabeer cikin matsanancin fushin dake nuna gab yake daya doki najeeb din.

Shiko najeeb a gigice ya ɗago yana kallon kabeer yace bakinsa na rawa.

"Kabeer salma bazata mutu ba,salma rayayyace batayi kala da mutiwaba,kar ka kuma alaƙanta tata da mutuwa"

"dallacan yimin shuru kai har kanada bakin magana yanzu,bayan kasa mahaifinta kuka,ita kuma gatacan rai a hannun Allah ,ay wlh ko hakkin hawayen mahaifin salma najeeb bazaka zauna lafiya ba,ace ayi mutum kamar jinin firauna,wacce irin maganace banyimaka akan salma ba,meye ban faɗa maka ba,amman dan tsabar bakasan darajar manyaba ina hanaka magana ƙara ɗaga murya kakeyi kai ga isasshe,wlh kanka kama,ba ruwan kabeer,kuma wannan hawayen da kakeyi,wlh kashirya,seka zubar da dubunsu anan gaba"kabeer ya fadi cikin kakkausar murya.

Najeeb ya kasa magana ware ido kawai yakeyi,yanaso ya hango abinda yayi ba daidaiba a maganganunsa da baban salma,amman shi a iya ganinshi,ba abinda yayi gaskiyar abinda ke ransa ya faɗi.

Har suka isa Abuja najeeb bedena kuka ba,shi kuma kabeer bedena zazzaga masa masifa ba,ƙarshema a bakin titi yasaukeshi,se taxi ya hau ya ƙarasa gidanshi.

Salma ko,likitocin sunyi nasarar daidaita numfashinta,sede ta kamu da ciwon zuciya me tsanani.

Ummanta se kuka takeyi,tana Allah wadai da najeeb,da yaudarar dayazo yay musu.

koda sahabi yaji abinda yafaru jiyayi kamar yay tsuntsu yaje yasami najeeb yaci mutuncinsa,sosai ranshi ya ɓaci.

Haka sukai ta jinyar salma,har tsawon watanni uku a asibiti sannan ta samu sauƙi aka sallamosu.

Tunda ta dawo gida sam batason hayaniya,ko hira ta daina yi da kowa kullum tana ɗaki tana tunani,bata taɓa tsammanin najeeb ze tozartata da ita da iyayentaba,segashi yashayar da ita mamaki,tunda yasanya mahaifinta kokawa a dalilinsa.

tsanarshi ce me girma ta mamaye saman zuciyarta,jitake kamar ta kasheshi.

haka rayuwa taci gaba da tafiya,yayinda najeeb yazama kamar wani mahaukaci,ga kabeer ya fita a harkarsa ko a waya yasashi a black list bashida ikon kiranshi.

Salma itama koya kira layinta sede ace baya ayki,sabida tajima da yarda layin.

yau da sassafe ya shirya yanufi gidan kabeer,sede yasha mamakin,samun mummunan labari agurin megadin gidan nacewa kabeer sati guda kenan da barinshi gidan,sabida ammishi transfer daga Abuja,amman besan inda ya koma ba.

jiri ne yafara ɗibar najeeb ,adaddafe,ya shiga mota ya koma gida.

koda ya isa gida kuka yake kamar yaro ƙarami,ji yake kamar yabar duniyar,yanzu ina ze nemo kabeer yabashi haƙuri su shirya?.


kimanin watanni takwas kenan da faruwar lamarin.

Inda mahaifin salma ya matsa mata akan tafito da miji shi yagaji da ganinta ahaka,inba hakaba ze kaita ƙauyensu ya aurar da ita sadaka.

Sosai batun ya ɗaga mata hankali,dan zuwa lokacin bata da saurayi.

Cikin hukuncin Allah ta haɗu da wani kamal,abokin sahabi,suka fara soyayya dashi,ba laifi tanason kamal shima yana sonta.

Har iyayenshi sunzo antsaida maganar auransu,murna gurin salma baa magana,dan dama zaman gidan ya isheta sabida sa'anninta duk sunyi aure sun haihu se ita tarage agida.

Ranar ɗaurin aure jamaa ba masaka tsinke dangin ango da amarya kowa ya hallara,anɗaura aure lafiya,kowa se murna yake.

wani mutum ne yaja mahaifin kamal gefe yamasa kuskus a kunne.

Ayko tuni mahaifin kamal yafara balai akan dole kamal seya saki salma.

koda aka tambayeshi,dalili se cewa yayi ay tsohuwar karuwace,kuma tsohuwar ƴar safarar cocaine,dan haka baze gurɓata zuriar shi da ita ba.

Haka ya tasa kamal akan dole seya saki salma,haka kamal yana kuka yarubuta takardar sakin yabayar.

Koda labarin ya isa cikin gidan su salma mahaifiyarta rushewa taƴi da kukan takaici.

itama salma sanda aka bata takardar sakin sumane kawai batayiba amman kuka tayishi ba adadi,Allah ya isa ko tajawa najeeb ita tafi kwandon dubu,dan shine yafara yimata tambarin karuwanci gashi nan yana binta.

Haka taro watse kowa se gulma yakeyi.


Tundaga wannan lokacin,mutane sunfi,shida dasuka fito neman auranta ana fasawa in sukaji labarinta,salma tarasa inda zata sa kanta duniyar tamata zafi,kuka yanzu tayishi har ta dena.

Tacire aure aranta dan ko kauyansu da mahaifinta yakai tallanta sadaka bawanda ya amsa sabida sunsami labarinta.

wasa wasa ko fita seda ta gagari salma sabida da zaran ta fita yara sukw binta suna jifa wai ga karuwa ga yar cocaine.

Bata da sakat ko mahaifiyarta tadena shiga taro,sabida da zaran tashiga zaa fara yada mata da habaici.


Yau kabeer ne yakamo hanya zuwa gidan su salma dan yasake ba mahaifin salma haƙuri,koda ya iso ƙofar gidan,parking yayi agefe,yana shirin fitowane,ya hango wata budurwa yara sunbiyota da gudu suna mata waƙar,"ga yar cocaine taƙi aure,waze aura?se ɗan banza,waye banzan?me bin mata"haka yaren suke cewa se jifanta sukeyi har sun fasa mata goshi,sun yaga mata hijabi,

koda suka ƙaraso kusa dashi seyaga ashe salmace yaran suka biyo,da gudu tashige gidansu,sannan yaran suka juya,da sauri kabeer yakira wani yaro me wayau acikinsu yatambayeshi.

"Abokina me wannan tamuku kuke mata waƙa haka kuna jifanta?"

dariya yaron ya kwashe daita sannan yace.

"wannan dakake gani,sau bakwai ana taruwa ɗaurin auranta ana fasawa,wanima seda aka gama ɗaurawa aka saketa,sabida ansamu labarin ashe tsohuwar yar cocaine ce kuma tsohuwar karuwa,sata kuwa ko ɓera albarka"

Hasbunallahu waniimal wakil,itace kabeer ya furta da ƙyar,sallamar yaron yayi yakoma cikin motarshi yakife kanshi akan sitiyari yana kuka,na tausayin salma da iyayenta.

"ina najeeb zekai alhakin salma da iyayenta"itace tambayar da kabeer yayiwa kanshi,jiki a sanyaye yaja motarshi yabar ƙofar gidan yana kuka na tausayin wainnan masoya dake cikin jarabtar ubangiji,yanajin haushin najeeb matuƙa amman yasan ba laifinshi bane haka Allah ya tsaro musu,amman dole zeyi iya bakin ƙoƙarinshi wajen ganin yashawo kan matsalar.


muje zuwa

surbajo for life.



Post a Comment (0)