Ƴar Bautar Ƙasa 21

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻🙆🏻

*DUK WANI MASOYINA YATAYANI JAJE WLH YANZU HAKA ZUCIYATA BUGAWA TAKE DA ƘARFIN TSIYA,INADA DARI BAKWAI A WAYATA,TO KUMA DATAR DUBU DAYA NAKE SAWA,SENAJE TA MOBILE BANKING ZANYI RECHARGEN NA 300 KUNGA YAZAMA DUBU DAYA KENAN,TO WLH TASHIN HANKALIN DAYA SAMENI BAZE MISALTUBA,MEMAKON INSAKA DARI UKU SENASA DUBU UKU,WLH BAN LURABA SEDA BANKI SUKA TUROMIN ALERT,INA CIKIN TSAKA ME WUYA😭😭😭😭😭😭😭ATAYANI DA ADDUA ALLAH YABANI HAƘURIN JURE KADDARAR DATA FADAMIN,DON ALLAH*

*Wannan shafin nakine masoyiyata,Allah yakara daukaka,yakareki daga sharrin duk wani abun ki,MAMAN AHMAD(MARDIYYA KAOJE)MARUBUCIYAR MUMTAZ,CHAIR LADY SURBAJO NA GAISUWA🤝*


*21*


Kai tsaye gida kabeer ya wuce,matarshi a ruɗe ta taryo shi,tana tambayarshi abinda yafaru dashi taga yana kuka.

Be ɓoye mata komai ba yasanar daita,itama rushewa tayi da kukan na tausayin salma dan tafijin tausayinta.

Sati guda tsakani,kabeer ya ɓoye number yakira najeeb,dakyar ya ɗauka,jin muryar kabeer ne yasa yamiƙe zaune yana faɗin.


"haba friend yanzu har abun yakai ga haka ka gudu kabarni bacin kasan banajin daɗin rayuwa idan baka?"

"dalla yimim shuru se zuba yake kamar famfon daya lalace,niba wannan ce tasa nakiraka ba,tambayarka zanyi,yanzu ka amince kanason salma ko baka aminceba?"

Shuru najeeb yayi kanshi na mishi zafi zuwacan de yadaure yace.

"Don Allah barrister kada kabari salma tashiga tsakanina dakai,dan wlh azahirin gaskiya ni bana son salma bantaɓa sonta ba kuma bazan taɓa ba har abada,nide kawai nasan ina jin tausayinta"doctor yaƙarasa maganar yana kuka.

kabeer bece masa komaiba yakashe wayarshi,koda najeeb yaji yakashe wayar wani kukan ne yasake ƙwace masa.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya,najib cikin tashin hankali,salma cikin tsana da tsangwama ta mutanan gari.

gaba ɗayansu sunyi baƙi sun lalace,bama kamar najeeb wanda gaba ɗaya yazama tamkar mahaukaci kuma ya rasa meke damunsa,ba irin gwajin cututtukan da beyiwa kanshiba amman results ɗaya yake samu,zuciyar shi nason wani abu.

Amatsayinshi na likita yasan matsalace babba to amman yarasa gano abinda zuciyar tashi takeso bare yabata.


Kabeer ne zaune agaban mahaifin salma suna tattaunawa,da ganin yanayinsu kasan sunɗan jima da fahimtar juna.

(abinda me karatu be saniba shine,kabeer tsawon wata guda kabeer ya kwashe yana zuwa gurin mahaifin salma yana bashi haƙuri,)

murmushi mahaifin salma yayi sannan yace.

"kabeeru kenan,to ay ko wani kazo nemawa auran salma zan bashi bare kuma kai da kanka,dan haka ka kwantar da hankalinka,inde kashirya kaje kasanar da magabatanka,azo ayi maganar,amman katabbatar kafaɗa musu komai game da salma".

godiya kabeer yayi sosai,daganan kai tsaye katsina yawuce gurin iyayensa,yamusu bayanin komai be ɓoye musu ba.

Dayake mahaifinshi malami ne me tsoron Allah,be ƙi ba.

Sati guda tsakani iyayan kabeer sukazo aka tsaida maganar,suka biya sadakin salma,

Bayan tafiyarsu mahaifinta shima yaje yayi bincike akatsinan yatabbatar da mutanen kirki ne

Wata guda tsakani,jamaa suka taru domin shaida ɗaurin auran salma da kabeer,

yan unguwar se gulma sukeyi,sabida suna ganin shima auran fasawa zaayi,sede ga mamakinsu anɗaura aure lafiya antashi bawani tashin hankali,ataƙaice ma har dangin angon sun koma gida.

Anata ɓangaren,salma kuwa,ta ɗauki auranta da kabeer da matuƙar muhimmanci ko kaɗan bata ƙin auran,sabida ko ba komai yacireta daga ƙuncin datake ciki.

Haka aka cigaba da shagalin biki kowa se murna yake,karfe huɗu aka kawo motar ɗaukar kaya,akaje aka shirya gidan amarya a unguwar malali GRA dake kaduna sabida kabeer dama kaduna yadawo da aykinshi,yayin da gidan uwargidanshi kuma yake a gomna road.

Yasha fama da Aisha matarshi kamin ta Amince ya auri salma.dan cewa tayi sede yasaketa.

Gidan amarya ba laifi yayi kyau sosai,daidai namasu ƙaramin ƙarfi,duk da cewa gidan namasu babban ƙarfine amman iyayenta sunyi ƙoƙarin tsara gidan da abinda Allah ya hore musu.

ƙarfe takwas nadare,motocin ɗaukar,amarya suka iso,inda aka ɗauki amarya tana ta kuka zuwa gidan mijinta kabeer.

ikon Allah.

surbajo for life.



Post a Comment (0)