Ƴar Bautar Ƙasa 22


*🙆🏻Y'AR BAUTAR K'ASA*



Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*22*


Haka ƴan kai amarya suka watse suka barota tana ta kuka.

Misalin sha ɗaya na dare ango yashigo ɗakin shi kaɗai,hannunshi ɗauke ɗa ledar kaji.

Sallamah yayi yashiga,bakin gadon yaje yazauna,yayi shuru,ita kuma se kukan ta takeyi.

Zuwa can de yadaure ya matsa kusa da ita,mayafin kanta yacire yajawota jikinshi yafara rarrashinta,da kyar yasamu tayi shuru,

Dakanshi yaɗauko plate yazuba kajin yadunga bata abaki har ta ƙoshi,daga haka brush sukayo da alwala sukayi sallah sannan suka kwanta.

Jawota jikinshi kabeer yayi yarungume sukayi bacci.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya,kabeer kullum cikin nuna ma salma soyayya yake ba abin data nema tarasa,itama sosai take nuna masa kulawa,

Tuni yase mata mota yasiyawa iyayenta gidan dasuke ciki yasa aka gyara masu gidan sosai,

Rayuwa tayiwa salma daɗi sede abu ɗaya ne yake hanata jin daɗin giɗan mijin,shine rashin kusantarta da kabeer bayayi,ita kuma macece me ƙarfin shaawa,amman haka ta haƙura dan ko maganar bayaso tamishi,se ya ɓata rai yace mata shi badan haka ya aure taba,ganin ranshi na ɓaci Ne yasa tadena yimasa magana ta koma faɗawa Allah damuwar ta.

Tuni salma tamance da wani najeeb arayuwarta.

Anashi ɓangaren najeeb yakoma kamar mahaukaci ko aski bayayi gashi duk yacika masa fuska bashida natsuwa duk a firgice yake.

Yanzu sauƙinta ɗaya suna waya da kabeer harma yabashi address din gidan shi dake kaduna.

Yaude Abujar tayiwa najeeb zafi dan haka shiryawa yayi yanufi Kaduna gurin Kabeer ko zeji daɗi.

Koda ya iso kaduna,se yacintsi kanshi dazuwa gidan su salma,koda ya isa yaci saa babanta yananan,dan haka gurinshi yanufa duk da sauyar gidan tabashi mamaki.

baban salma be gane najeeb ba seda najeeb ya gabatar da kanshi.

Da sauri yajawo shi jikinshi yarungumeshi yana faɗin.

"najeebullahi najima inason ganinka amman Allah be nufa ba se yanzu,kayi ciwone naga ka lalace haka?"

Kuka najeeb ya rushe dashi yana ƙara rungume baban yana neman gafarar shi abisa rashin kunyar daya masa.

Dariya baban yayi sannan yace.

"najeebullahi,bakamin laifiba,ko fushin danayi dakai rainane ya ɓaci ba komai ba,amman yan zu bana tare da ɓacin ran komai,nayafe maka tun tuni"

har cikin gida yashigar dashi gurin mahaifiyar salma dakyar ta amince tayafe mishi,haka shima sahabi dakyar ya amince,daganan ne najeeb ya buƙaci ganin salma,itama yabata haƙuri,cikin faraa mahaifinta yace.

"wai ay salma shekararta guda kenan agidan mijinta,ay tayi aure"

Jirine yafara ɗaukar najeeb kamin wani lokacin yazube ƙasa sumamme,a gigice suka ɗebo ruwa suka shiga yayyafa masa,be jimaba ya farko yana wani gunjin kuka ,ƙafar mahaifinta yariƙe yana kuka yace.

"baba meyasa ka aurar da salma? meyasa baba?"

tambayar sosai tabashi mamaki,amman se yace,

"sabida ta isa aure shiyasa na aurar da ita,danko calender ce ita watarana zan gaji da kallonta nayaga kona ƙona"

Najeeb kasa magana yayi,cikin fushi yamike yafice daga gidan suna kiranshi amman ko waigowa beyiba yaje yashige motarshi yatada daita yabar anguwar.

yana tafe yakira kabeer yace mishi gashinan zuwa gidan shi.

Sosai kabeer ya firgita da zuwan na najeeb,kamin yayi wani yunƙuri najeeb ya iso gidan.

jin nucking yasa kabeer daurewa yaje ya buɗe masa ƙofar,yana buɗewa najeeb yarungume kabeer ya rushe da kuka dakyar kabeer yajashi zuwa cikin falon suka zauna,cikin kuka najeeb ke faɗin.

"kabeer iyayen salma sun cuceni,sun aurawa wani salmata,kabeer ina zan saka rayuwata,?"yaƙarasa maganar cikin matsanancin kuka.

a daidai lokacin salma tashigo falon sabida tajiyo sautin kuka daga ɗakinta,sanye take cikin riga da wando three quater tayi kyau sosai,har ta shigo falon basu saniba.

Najeeb ne yafara ɗsgo kanshi arazane sabida yajiyo ƙamshin salma,koda ya waigo ido cikin ido sukayi shida ita,azabure ya miƙe ya nufeta tana ja da baya da sauri kabeer yace.

"kada ka kuskura kayi gangancin taɓamin mata"ya faɗi sanda ya ƙarasa ya rungumo salma jikinshi,ita kuma se wani ƙara shigewa jikinshi takeyi.

*Tassssssssssss*

Najeeb yaɗauke kabeer dawani gigitaccen mari,sannan yaje yacukumi kwalarsa,yace.

"kada ka kuskura kasake maimaita wannan kalar wasan agabana,nakiran salma matarka"

Tassssssssss.

yaji shima an ɗaukeshi da mari,koda ya waiga salmace sannan tace cikin ɓacin rai.

"wannan ne ganganci mafi muni dazaka kumayi agabana na marin mijina,kai waye dazaka shigo har gidanmu kana cimana mutunci?"

Tsananin mamaki najeeb yakasa magana bakinshi rawa yake kamat mazari,da kyar yace.

"kina nufin kabeer shine wanda kika aura?"

"kana mamakine?"kabeer yabashi amsa.

"kabeer kagama dani duniya da lahira,bani da wani abu dazan iya yimaka,kayimin abinda ko maƙiyina baze yimin ba,duk wani abu dazanyi maka baze gogemin duhun dakasa azuciyata ba"

Be jira abinda zasuce ba yafice da gudu ya faɗa motarshi,da gudu kabeer yabi bayanshi dan yasan komai ze iya faruwa inyabarshi yatafi,sedr kamin ya iso najeeb yafice da mahaukacin gudu,daga gidan,

Da gudu kabeer ya koma cikin gidan ya ɗauko key din motarshi shima yatada yabi bayanshi,

Gudu suke sosai yayinda najeeb ko gabanshi ba sosai yake ganiba,a haka har suka iso gadar Abuja junction,wanda najeeb yajima da sumewa a motar dan haka,kabeer se gani yayi sunyi taho mu kara da tirela,wanda hakan yajanyo motar najeeb ta faɗa ƙasan gadar wacce ƙasanta titine,wata tirelar ce tayi tafiyar yaji da motar ta wancakalar da ita gefen titi.

Ihu kabeer yakeyi,iya ƙarfinsa,yafito daga motarshi,da gudu ,jamaa suka riƙeshi dan kan titi yahau be saniba.

Da ƙyar aka ciro najeeb acikin motar,wanda dagani base an faɗiba babu alamun rai atattare da
Post a Comment (0)