Ƴar Bautar Ƙasa 23


*👩🏻‍💼YAR BAUTAR KASA*

Zahra Muhammad Mahmud

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*23*

Emergency aka tafi da gawar najeeb,wacce ke ta faman zubar da jini.

Kabeer ko ihu yakeyi gaba ɗaya yafice daga hayyacinshi,

Likitoci ne akan gawar najeeb suna bincike,cikin ikon Allah sesukaji jijiyar bayan kunnenshi na bugawa.

Da sauri suka jawo kayan ayki suka shiga ceton ranshi,inda cikin nasara bugawar zuciyarshi yadawo,amman da sauri da sauri,alamar dake nuna zuciyar bata da lafiya.

Tsawin awanni uku numfashin shi yaƙi daidaita,duk wani abu da suke tunanin yimishi sunyi amman abun yaci tura.

Gwaje gwaje suka shiga yimasa,anan suka fahimci akwai abinda yakeso be samuba,dan haka da sauri suka nufi kabeer,wanda ke birgima akasa kamar yaro,suna zuwa ɗaya daga cikinsu yace masa.

"we dont have enough time,only one hours remain for your patient,based on our investigation,we find out that there was something he needed on this earth urgently,and he couldn't obtaind it,but if you know the actual thing he needed,you are free to bring it right now,Becouse that is the only solution to save his life"

Tunda likitan yafara magana kabeer yake gyaɗa kai kamar ƙadangaren,yana gama saurarar su yajuya da wani mahaukacin gudu,ya faɗa motar shi,ko murfin be jira yarufe ba ya finciketa da mahaukacin gudu se a hanya ya rufe murfin.

Cikin minti goma ya iso gidan shi,koda yafita be jira yarufe motarba,ya ruga da gudu zuwa cikin gidan.

A falo yasami salma se kuka take yi fuskarta tayi jazir,yana shiga tamiƙe da sauri tace.

"ya kashe kanshi ko?,don Allah kasanar dani a halin dayake ciki jikina yana bani wani mummunan abu yasami doctor"taƙarasa maganar tana kuka me nuna zuciyarta nacike da fargaba.

Jawota yayi da ƙarfi yana shirin ficewa da ita waje,da sauri ta ƙwace takoma gefe tace.

"ina kakeso ka kaini?"

Hawaye ke zuba a idon kabeer kamar ruwa yace.

"salma gurin najeeb zan kaiki"

"a matsayinsa nawa agurina dazaka kaini gurinshi"

"salma najeeb yana sonki,kuma kema kina sonshi don Allah ki taimakeni kar na rasa najeeb,in wani abu yasameshi bazan yafewa kaina ba"kabeer ya faɗi yana kuka.

"tun wuri ka gyara maganarka ni ba son najeeb nakeba tausayins kawai nakeji,ni mahaukaciyar inace zanso mutumin da besan mutuncin iyayena ba?"

"ƙaryane salma,wlh kinason najeeb,kullum dasonshi kike kwana kike tashi,najeeb yana cikin halin buƙatarki akusa dashi,kitaimakemu"

"kabeer na fahimci bakasan darajar auren dake kainaba,shiyasa kakemin zancen wani ƙato"

"salma nifa na aurekine dan najeeb, ina tsoron wani ya aureki,lokacin da najeeb ya waiwayeki kuma yarasa ki,shiyasa namasa adashin gata dake wanda yaune ranar daze kwasa,salma komai namiki namikine dan son da najeeb yake miki,inde akan aurena dakene yasa kikace bazakije gurinshi ba,salma nasakeki saki uku "kabeer ya furta yana kuka.

Arazane salma take kallonshi bakinta na rawa tace.

"what do you mean Kabeer,ashe duk soyayyar daka nunamin ƙaryace?kayine dan abokinka,kabeer banmaka laifin komaiba kasakeni,saki irin na wulaƙanci me naimaka kaida abokinka dakukeso kuga kun jefa rayuwata cikin ƙunci?"

"salma akan najeeb zan iya yin komai,ina nufin komai"ya faɗi cikin ɗaga murya.

hannunta yaja tasake kwacewa tana kuka.

Cikin tsawa kabeer yace.

"Salma fitar najeeb dazu daga gidan nan,sunyi karo da tirela,inda ta wurgoshi shida motarshi ƙasan gadar Abuja junction,inda wata tirelar tasakeyin tafiyar yaji dashi da motar tashi,ankaishi asibitin garden city,likitoci sunyi iyayinsu,najeeb yayi numfashi amman yaƙi yi,salma likitocin sun shaidamin awa ɗayace taragewa najeeb a duniya matuƙar baakai masa abinda yakeso kusa dashiba,ze mutu,kece wacce najeeb yakeso batare dayasan yana yi ba,saura minti goma shabiyar yarage najeeb yabar duniya,nasan zakiyi alfahari da cewa najeeb yaceto rayuwarki daga gidan yari,shi kuma kinyi sanadin turashi lahira"ya ƙarasa maganar yana kuka.

Da wani mahaukacin gudu salma tafice daga falon,binta yayi abaya,motar dayazo acikinta taje tashige,ƙafa ba takalmi,kai ba ɗankwali,sanye da wando three quater da riga armless.

kamin kabeer ya ƙaraso taja motar tafice daga gidan da mahaukacin gudu.

Ta nufi Asibitin garden city dake kaduna,inda aka kwantar da najeeb.

Koda kabeer ya iso yaga tafice wata motar yaje yashiga shima ya fice da gudu,sede shi ba Asibitin yanufa ba gidan iyayen salma yanufa.

Tofa🙆🏻

muje zuwa,akwai bidiri.

surbajo for life.

Post a Comment (0)