Ƴar Bautar Ƙasa 24


.*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*


Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

*duk meson ayi adding wata number agroup pls yaba wata admin din baniba,ni sim card dina yacika da numbers,masu bina naturo yar bautar ƙasa ta pc kuyi haƙuri ku tambaya a group bana turawa ta pc,ku kuma masu shi don Allah in antambaya kubayar ni uzuri yamin yawa,pls*


*24*



Tana isa asibitin,tayi parking,bata tsaya kulle motar ba ta ruga da gudu zuwa cikin asibitin kamar mahaukaciya,dama gata akwai gashi.

Wata nurse ta tare tana tambayarta najeeb,ayko ba musu takaita ƙofar ɗakin dayake ciki.

Tura ƙofar tayi da gudu tashige cikin ɗakin,da sauri likitocin suka waigo suna kallonta,itako ko kallonsu batayi.

Ƙarasawa tayi jikin gadon najeeb ɗin tana kallon yadda aka naɗe jikinshi da bendeji sabida raunukan dayaji,ga karaya da yayi a ƙafarsa,duk wanda yaga najeeb awannan yanayin se ya tausaya masa bare salma masoyiyarsa,

Kuka take kamar wata zararriya,hannunshi ta kamo tana kiran sunan shi cikin kuka,amman shuru bemasan tanayiba.

Naurar jikinshi ce tafara ƙara alamar lokacin da aka ɗiba yayi,gaba ɗaya likitocin sun rude,

Faɗi suke,"we lost him"

A gigice salma take kallonsu,dubanta takai fuskar najeeb,da sauri takifa fuskarta akan fuskarshi,ta haɗa bakinta danashi tashiga hura mishi iskar bakinta daƙe shiga cikin huhunshi.

Yitake iya ƙarfina tana gunjin kuka.

Tarin da najeeb yafarayine ya maido da hankalin salma dana likitocin,da sauri suka janye salma suka samasa oxygen a bakin.

Da kyar yake zuƙar numfashin,salma se kuka takeyi gwanin ban tausayi,likitocin se alokacin suka fahimci ciwon so ne yskama najeeb me tsanani.

shiko kabeer yana isa gidan su salma shima ko ƙofa be rufeba ya ruga kofar gidan inda babanta ke zaune shida wasu dattawa suna hira.

Da gudu kabeer yazube agabanshi yana haki yana kuka yace.

"Baba don Allah karka tambayeni dalili,nasaki salma saki uku,batare dana ɗora mata iddah ba,a iya zamana da ita,najeeb yasamu labarin ni salma take aure,yabar gidana afusace sanadin hakan yayi taho mu kara da tireloli har guda biyu,yanzu haka yana asibiti,cikin halin mutuwa ko rayuwa,baba in har ka amince masoyine ze ita ceto masoyinsa daga gidan yari,baba ka aurawa najeeb salma,idan har ka amince da natsuwa da tarbiyyar najeeb baba ka aura masa salma,in babu salma arayuwar najeeb baba mutuwa zeyi,katausayamin nida aminina ka aura auren salma da najeeb yanzu"kabeer ya fadi cikin kuka.

"Jamaa salati goma ga Annabi"cewar baban salma.

"S,A,W"Sauran mutanen suka amsa,

Hannu yasa a aljihunsa yaciro kudi dubu biyar yamiƙawa kabeer,kabeer hannu na rawa ya karɓa,

"ni malam hadi ina nemawa ɗana najeeb auren salma agurinka"

Bakin kabeer har rawa yake yace.

"Ni kabeer naba ɗanka najeeb auran salma abisa sharudda kamar haka"

Nan aka lissafo hakkonkin aure,baban salma yace.

"na amsa masa"

kamin wani lokaci me tsayi angama ɗaurin auren najeeb da salma,kabeer rasa bakin godiya yayi da gudu yamiƙe yanufi motarshi da sauri baban salma da sahabi suka bishi yaja suka nufi asibitin.

Koda suka shiga ɗakin salma ce zaune kan kujera ta kifa kanta akan goshin najeeb hannunta riƙe da hannunshi,gashin kanta ya zubo yarufe fuskokin nasu,

Kabeer ganinsu ahaka seji yayi wasu hawaye na farinciki sun kama shi,yau yayiwa najeeb abinda ze godemasa,yayiwa najeeb abinda har ya mutu baze manta dashiba,yayiwa najeeb abinda ze dauwama cikin farin ciki,wato aura masa salma.

Har suka shigo salma batasan sun shigoba hankalinta nakan najeeb,tana tunanin yaushene ze farka.

Mahaifin salma da sahabi seda suka koka ganin halin da najeeb yake ciki adalilin salma.

jansu waje kabeer yayi,suka zauna,wayarshi ya dauko yakoma gefe yakira mahaifin najeeb.

Bayan sungaisa,kabeer yakwashe komai yasanar da mahaifin najeeb ɗin tun farkon haɗuwar najeeb da salma har zuwa yanzu da aka ɗaura musu aure.

sosai hankalin mahaifinshi yatashi,anyi saa yana ƙasar,dan haka yashaidawa kabeer nan da awa biyu ze iso.

Suna nan zaune jugum jugum,har awa biyun ta cika,mahaifin najeeb ne yashigo Asibitin da gudunshi.

Da sauri kabeer yatarbeshi,yakaishi ɗakin da najeeb ɗin yake,sede har lokacin gashin salma yarufe fuskar najeeb baa gani yayin da itama tata baa gani,

Kabeer ne ya ƙarasa kusa da kunnen salma yace mata ta tashi ga mahaifin najeeb.

Hannunshi ta saki amman se taji shi yayi sauri yariƙe nata,da sauri ta ɗago kanta tana duban fuskarshi,

ba salma kowa seda yayi mamakin ganin idanun najeeb a buɗe yana kallon salma hawaye nazuba ta gefen idonshi.

Da sauri mahaifinsa yamatsa kusa dashi yana masa sannu.

Binsu kawai yake da ido amman ba baki.

likitocinne suka zo suka korasu waje,sannan aka canjawa najeeb ɗaki zuwa wani na musamman wanda babu me shiga sede me jinyarsa wato salma.

Guri suka samu suka keɓe aka sake maimaitawa mahaifinshi komai,ga mamakinsu be ji haushin aurawa njeeb salma ba,sema godiya daya dunga yiwa mahaifin salma harda hawayensa.

Muje zuwa.

Surbajo for life.


Post a Comment (0)