Ƴar Bautar Ƙasa 25

*👩🏻‍💼Y'AR BAUTAR K'ASA*



Zahra Muhammad Mahmud


DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION


*PLS MESON BOOK DINA YATAMBAYA A GROUP,NI BANA TURAWA PC,SABIDA NAYI ME WUYAR TUNDA NATURO GROUP,ADDING NUMBERS KUBA WASU ADMINS DIN KOWANNE GROUP DINA AKWAI ADMIN KUBASU,NI WLH UZURI YAMIN YAWA,KU KUMA ADMINS IN ANBAKU KUSA KA,AMMAN ADMIN DIN SURBAJO HAUSA NOVELS(MY SCRET)KARKIYI ADDIN DIN KOWA ACIKIN SA,AMMAN SAURAN AYI,PLS🙏*


*25*


Waya Alhaji hassan yayi yasanar da hajiya kaltum halin da ake ciki,harda auren da aka ɗaurawa najeeb din.

A wayar harda kuka tayi na tausayin najeeb din,tana kashe wayar tamiƙe afusace tana kai kawo.

"najeeb kayi kuskure daka faɗa tarkon son wata ƴa mace baniba,wlh inde sunana kaltum,sena hanaka jin daɗin auran da kayi dani kake magana"sune kalaman sa hajiya kaltum ke furtawa cikin fushi.


Salma kowa yaganta se yaɗauka tare suke ciwon,dan itama bakinta ya kulle tadena magana sede ido,babu yadda baayi daita ba akan taje gida tabar kabeer yakula dashi amman fafur taƙi amincewa,dan ko ma ta miƙe zata yi wani abun sede tayi da dabara dan hannun najeeb riƙe yake da hannunta kowannen motsinta akan idonshine,sede inyayi bacci ne take da lokaci.


Hajiya kaltum tazo dubashi,yayinda taga salm seda numfashinta yakusa tafiya,sabida ganin ƙirar da Allah yay mata,take taji kishi da tsanarta sun baibaye zuciyarta,inda ta ayyana ko tawacce hanya seta rabasu.

Wasa wasa seda najeeb yayi wata uku a Asibiti sannan yafara magana,amman be fiye yiba yafison yayi shuru.

Idan kabeer yazo dubashi rufe idonshi yakeyi sabida ji yake kamar zuciyarshi zata fito inya kalleshi,yatuno yanzu fa kullum seya kwanta da salma seyaji kamar yakasheshi.

kabeer yasan najeeb na kishi dashine shiyasa be masa magana,dan haka be damuba illah dariya ma da abun yabashi.

Mahaifin najeeb ganin yasamu sauƙine yasa yakoma kano,yasa aka,ginawa najeeb plat me kyau da tsari acikin gidanshi,abisa jagorancin umarnin da hajiya kaltum tabashi,sabida da awaje ze gina masa,se tsautsayi yasa yafaɗa mata,ayko ta shiga ta fita.ba abinda baa zuba acikiba na more rayuwa,sannan dakanshi yaje kasuwa yasa aka haɗa lefe nagani na faɗa,dazeje duba najeeb din yakai gidansu salma da kuɗi milyan daya amatsayin dukiyar auren salma.

Yau aka sallami najeeb a asibiti,babu mecewa yayi ciwo,yawarke garas.se ƙafarshi dayake ɗan ɗingisawa

Tun da daɗewa yake so yasamu wanda ze tambaya meyasa salma take kwana agurinshi,amman yarasa wanda ze tambaya.

Tun safe kabeer yazo awata mota marcedez venz 4matic,fara,me baƙin glass anyiwa motar decoratin da kayan decorating,dasu balam balam kalar bulu da fari,number motar ansa,
*NAJEESAL* gaba da baya,se wani rubutu da aka rubuta happy marriage life najeesal.

motar se ɗaukar ido take gwanin sha'awa.

a daidai ƙofar fitowa daga reception din asibitin,yayi parking ɗinta,sannan ya shimfida bulu fin carfet,aƙasa zuw ƙofar tundaga bakin motar,shima karfet din an rubuta,happy marriage life najeesal da farin rubutu.

Shiga cikin Asibitin yayi lokacin,najeeb na zaune shuru yana kallon salma dake ta ƙoƙarin zuge zip din rigarta amman takasa,

Miƙewa yayi ahankali ya ƙarasa gurinta seji tayi yacire hannunta yaja mata zib din sannan yakoma ya zauna.

Kabeer ne yashigo ɗakin da sallamarsa,hannunshi riƙe da flawer me kyau itama blue da fari,najeeb na ganinshi yakauda kanshi gefe.

Dariya kabeer yayi ya ƙarasa gurinshi yace.

"Ango kasha ƙamshi,ina tayaka murnar fara sabuwar rayuwa Allah yasanya alkhairi abokina"ya miƙa masa flower din.

kan najeeb ne ya ɗaure dajin maganar kabeer,kallo yabishi dashi,kabeer ganin najeeb beda niyyar amsar flawer ne yasa yakamo hannunshi yasaka masa.

Sannan yace su taso karsuyi dare a hanya.

Salmace tafara miƙewa,amman shi najeeb beda niyya ganin hakane yasa salma matsawa kusa dashi ta miƙa masa hannun ta alamar yakama.

shashin da kabeer yake ya kalla sabida yanajin tsoron riƙe hannunta agabanshi.

gyaɗa masa kai Kabeer yayi dan haka, kama hannun nata yayi ta miƙar dashi tsaye suka fice daga ɗakin.

kowa se barka yake masa nasamun sauƙinsa.

koda suka iso bakin ƙofar fita sosai abun yaba najeeb mamaki ganin nurse din asibitin tsaye gefe da gefe na asibitin sina watsa flawer akansu,

*NAJEESAL* me hakan ke nufi cewar najeeb.

Haka suka taka har gurin motar aka buɗe musu bayan motar suka shiga,aka dunga watsawa motar flawer,kabeer ya shiga yajasu,zuwa gidan su salma.

Nasiha baban salma da mamanta suka musu,se alokacin najeeb ya fahimci an ɗaura masa aure da salma ne,

kallonsu yake kamar wawa,danshide yasan ay se anyi iddah ake ɗaura aure tosu nasu meyasa aka ɗaura bayan salma batayi iddah ba?.

Kanshi a ɗaure yafito ƙofar gidan,shi besan ma me zeyiba,kowa yace su ɗaura mishi aure da ita oho,shifa ba sonta yakeba,amman ba komai,ya amsa amman se ta gane kurenta dan yafahimci itace tace tana sonshi.

Salma se kuka takeyi haka aka rakota zuwa mota da kayanta na sawa da kawo mata na lefe da kuma nasawarta na gidan kabeer,akasa a both din motar.

Key din motar kabeer ya miƙawa najewb yace yana dariya.

"ba wanda yafika sanin darajar salma dan haka nasan senafi kowa iya janta a mota,"ya miƙa masa key din.

amsa najeeb yayi rai aɓace dan haushin kabeer yakeji sosai.

shiga mazaunin direba yayi salma tashiga gefe aka kulle motar.

ƴan uwan salma mutum huɗu da,zasu rakata kuma suka shiga motar da kabeer yasa aka kawo masa yabi bayan najeeb abaya,suka kama hanyar kano raka ango da amarya.

Muje zuwa.


surbajo for life.



Post a Comment (0)