AZABAR MAZINATA

*AZABAR MAZINATA😱*


    Annabi (S A W) ya bamu labarin cewa A lokacin da yaje _(Mi'iraji)_ ya leka cikin wuta sai yaga wasu mutane tsirara an tattarasu a cikin wani ramin _Dagwalon Azaba_ wuta tana ci ta qasan su.
   Kuma mala'iku suna jibgarsu suna ci gaba da musu azaba.
   Sai ya tambayi mala'ika Jibrilu yana cewa: *YA JIBRILU WADANNAN SU WAYE NE?*
  Sai Jibrilu yace: *WADANNAN MAZINATA NE.*

   SAI ANNABI (S A W) Ya bada labarin cewa akwai wani irin ihu da kururuwa wanda "yan wuta suke yi in an bude musu *(Farjojin Mazinata).*
Kunji fa jama'a saboda tsananin wari da doyin Al'auran mazinata idan an bude shi dukkan "yan wuta sai suyi ta ihu suna yin kururuwa.
   Hakanan akwai wani ruwa mai bala'in wari wanda yake fitowa daga cikin al'auran mazinata idan ana gana musu azaba.
   Wannan ruwa shine ake ce mishi *(TEENUL KHABAAL)* Yana daga cikin nau'in abincin da " yan wuta suke ci a cikin wuta.
 
   Ya ku "yan uwa ina bamu shawari da mu guji zina da dukkan dangoginta domin zina babbar musiba ce.
   Amma wani abin takaici har akwai wadanda suke ganin in baka zina to kai ba ka waye ba, kai baka more ba, kai ba ka burge ba.
  Amma don Allah abin tambaya anan shine: _Don Allah menene abin burgewa a cikin sa6on Allah?_

  Allah ta'ala ya tsaremu da aikata alfasha yasa mufi karfin zuciyarmu.



```>>Ga mai tambaya ko neman karin bayani sai ya tinti6emu akan wannan lambar kamar haka 👉🏼(08108605876)



✍🏻 *Rubutawa*
_Ibraheem Khalil_

{08094000845}

Post a Comment (0)