ABDULKADIR SALADIN 04

4. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Kafin im fadi irin jidalin da gwamnatin Masar ta sha, kafin ta i wa wannan Mahadi, bari mu taba dan tarihinsa mu ga yadda ya tsiro.
Wannan dam bore da ya nada wa kansa Mahadi, sunansa Muhammed Ahmed. An haife shi a tsibirin Argo, kusa da Dongola. Iyayensa matalauta ne kwarai, sai dai sun ce su sharifai ne. Amma ko da ya ke mutane ba su musun cewa dangin Muhammed Ahmed sharifai ne, duk da haka ba su yarda suna ba su girman da a ke ba sharifi ba. Ubansa dai malami ne, yana karantarwa. Ya koya wa dan nan nasa karatu da rubutu tun yana yaro, kuma tun a lokacin nan uban ya mutu ya bar shi maraya. Amma Muhammed Ahmed ba ragon da ne ba. Ya ba da himma kwarai ga karatu. Ko ina ya tafi dalibta nan da nan sai ya yi tagomashi wurin malamansa sabo da himma tasa, da hazaka, da takawa.
Da ya balaga sai ya nufi Kahartum, a can ya zama dalibin mashahurin shaihun nan da a ke kira Sheikh Muhammed Sherif, wanda kakansa Sheikh Tayeb shi ya fara kafa darikar Sammaniyya. Ba a dade ba, Muhammed Ahmed ya yi kyakkyawan fice a cikin himmar darika, ya kuma zama mai biyayya kwarai ga shugaban darikar, Sheikh Muhammed Sherif. Bayan ya gogu sosai wajen ilmi da ibada, sai ya tashi ya koma wani tsibiri a Farin Nil, da a ke kira Tsibirin Abba. A nan ya shiga noma da karantarwa. Nan da nan ya sami 'yam mabiya suna tare da shi. Noman nan shi ya ke ci, sai kuma sadakar da masu shigewa ta garin kan ba shi. Wannan fa kullum ne!
Ran nan Muhammed Sherif, watau ubandakin Muhammed Ahmed, ya sha dansa. Da lokacin kaciyar ya zo, sai ya tara duk dalibansa don a yi bikin kaciya, yadda al’adarsu ta mutanen Sudan ta ke. Bayan sun taru, sai Muhammed Sherif ya ce suna iya yin rawa ko waka don nishadi da murnar wannan rana, babu kome. Duk zunubin da ke ciki, shi ya iya yafe musu. Shaihun malami irin Muhammed Sherif kome ya ce zai yi ba a musu. Amma Muhammed Ahmed, da ya ke shi na Allah ne, takiyi, sai ya ce waka da rawa bida’i ce, Allah kuwa ya hana bidi’a. Mutum kuwa, ko wane ne shi, ba shi da ikon yafe zunubin wani mutum kamarsa, Allah kadai ke yin gafara.
Da wannan zance ya kai kunnen Muhammed Sherif, sai ya dauka kamar Muhammed Ahmed ya tozarta shi ne. Ya yi hushi, gayan hushi, ya sa aka kira Muhammed Ahmed ya ce ya zo ya fadi dalilin da ya karyata shi. Ko da Muhammed Ahmed ya zo gaban malaminsa, sai ya sunkuyad da kansa kurum, ya yi ta tuba, ya yi ta tuba, amma Sherif ya ce ya tashi ya ba shi wuri, ba ya yafe masa har abada. Ya zage shi, ya zage shi, ya ce masa munafuki, lalatacce, mai neman ta da zaune tsaye. Ya fisshe shi daga darikar Sammaniyya. Zuciyar Muhammed Ahmed ta yi bakikirin, sai ya tafi wurin wani danuwansa ya ce ya yi masa sheba. Shi sheba wani dan ice ne a kan tsaga shi kamar gwafa, a garkama a wuya. Ma’anar haka, watau mutum ya nuna wa wanda ya yi masa laifi, da kuma sauran duniya duka, cewa lalle ya amsa laifinsa amma ya tuba matukar tuba. Sabo da haka da ya garkama sheba a wuyansa. sai ya zo ya fadi gaban Muhammed Sherif cikin ganiyar tawali’u, da kaskantad da kai, ga toka ya barbada a kansa, ya shiga tuba. Muhammed Sherif ko da ya dube shi sau daya, sai ya kau da kansa, ya kore shi, ya ce ban da dai maganar yafewa. Shi kam sun yi sallama ke nan duniya da lahira! Muhammed Ahmed ya tashi da dan gindi, ana binsa da kallo da karkiyar sheba a wuya, bai zame ba sai Abba, garinsu.
Ran nan sai ya sami labari Muhammed Sherif ya zo wajajen garinsu. Sabo da haka bai daddara ba dai, sai ya sake garkama sheba, ya kwashi gudu sai gare shi. Da ya je ya kama kafa ga manya mabiyan Muhammed Sherif. Suka kai shi gaban malam, ya sake gurfana a kasa, ya shiga tuba. Muhammed Sherif ya harare shi, ya daka masa tsawa ya ce, “Tashi ka ba ni wuri, munafuki, mara tsoron Allah, mai raina malaminsa! Lalle ka nuna gaskiyar maganar mutane da su ke cewa, ‘Mutumin Dongolawi Shaidan ne cikin sifar mutane.’ Ka nemi ka karyata ni, ka watsa jama’ata. Bace mini da gani, har abada ba na yafe maka. Wofi !”
Jin haka, hankalin Muhammed Ahmed ya tashi kwarai, ya ga in ya nace tuba wa wannan taliki, kamarsa, lalle zai sabi Ubangiji. Don yadda duk mutum zai tuba wa mutum danuwansa, ya tuba wa Muhammed Sherif. Tun da ko ya ki yafe masa, shi ke nan. Shi ma ya rabu da shi duniya da lahira, don kuwa ba shi ya halicce shi ba, ba shi kuwa da wuta, ba shi da aljanna. Sai ya ta da kansa, ya cire karkiyar shebar da ke wuyansa, ya kade rigarsa ya yi tafiyarsa. Ashe wannan rabuwar, wani sabon shafi ne Muhammed Ahmed ya bude wa kansa cikin tarihinsa na zaman duniya.
Yana komawa gida, sai ya fada wa danginsa duk yadda aka yi. Ya ce musu yau ya bar Mahammed Sherif, ya kuwa fita daga bin shugabancinsa cikin Sammaniyya. Sai ya je gun wani shaihi da a ke kira Shaihil Kuraishi, ya tabbatad da shi cikin jama’arsa, ya ci gaba da darikarsa a hannunsa. Shi Shaihil Kuraishi yana zaune a wani gari ne da a ke kira Mesalamiya. Lokacin da Muhammed Ahmed da dalibansa suka shirya za su tashi zuwa wannan gari, su yi caffa gun Shaihil Kuraishi, sai ga takarda daga Muhammed Sherif cewa Muhammed Ahmed ya zo ya yafe masa. Muhammed Ahmed ya ce, “Af, buleke ke nan, toshi a bayan salla!” Ya dauki alkalami ya mai da amsa. Ya ce ya ji sakonsa, amma shi bai ga laifin da ya yi har da za a yafe masa ba. Ya ce hasali ma ba daidai ne dan Dongolawi kamarsa, wulakantaccen duniya, ya zo har mutane su gan shi a gaban mai martaba irin Muhammed Sherif ba. Ya karya wa malam mutuncinsa ke nan. Maganar yafewa, a tafi ba ya so. Sai ya shirya ya nufi wajen Shaihil Kuraishi abinsa.
Nan da nan labarin wannan amsa ya watsu ko ina a Sudan. Mutane suka shiga mamakin yadda dan darika zai ki karbar yafewar shugabansa. Dalilinsa na kin karbar kuma ya bazu, cewa shugaban nan ne ya ratse daga turbar Allah, shi ya sa almajirinsa ya guje shi. Jin haka fa mutane suka kara na’am da Muhammed Ahmed, suka kara sonsa, girmansa ya karu a zukatansu. Ko wace jiha ka nufa a Sudan, tadin ke nan, nan da nan sunan Muhammed Ahmed ya watsu.
Ran nan sai ya roki Shaihil Kuraishi, ya ce yana neman izni ya je ya ga danginsa a Abba. Da isarsa gida mutane suka dinga ketowa daga ko ina suna zuwa neman tubarriki a gare shi. Suna cewa ga mutumin da ya ki kauce wa hanyar Allah, don tsoron zuciyar mutum. Daga Abba ya nufi Kordofan. A garuruwa, da kauyukan da ya ratsa duk kamar za a dauke shi a sama. Ya rika wayad da kan malamai wadanda ke daure cikin kangin bautar jahilci. Ya rika nuna musu cewa shugaban darika, ko wane ne shi, mutum ne kamarsu. Odojinsa ba su ne abin rikewa ba, odojin Ubangiji Allah, su ne abin a kiyaye. Shugaban da ya ce mutane su ratse turbar Ubangiji, a bi tasa, wannan zindiki ne, sai a guje masa. Ya rubuta ’yan kananan littattafai ya rarraba ga manyan mabiyansa. A ciki ya hore su bisa tashi tsaye su tsarkake addini, su fid da daudar camfi da al’ada, da suka gurbata shi. Ya ci gaba da cewa daya daga cikin manyan abubuwan da ke bata addini, ita ce hukuma, watau gwamnati. Ma’aikatan gwamnati suna shiga rigar iko suna wulakanta jama’a, suna kuma yin abubuwa masu raunana addini. Ya ce jama’a su bar karbar maganar malamai masu bin son zuciyarsu, su kuma daina jin zancen gwamnati! Ka ji farkon satirum Mahadi ke nan da gurbatar kasar Sudan. Bari mu ji yadda Muhammed Ahmed ya sami yin haka.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada


Post a Comment (0)