ABDULKADIR SALADIN 11

11. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Sai na aika aka kira mini Farag Effendi, da Wad Asi, da alkali, na fada musu yadda muka yi da Zogal. Suka ce har yanzu ba su gaskata shi ba sai ya rantse tukuna. Aka kawo Alkur’an ya je ya yi alwala, ya rantse. Bayan kwana uku shiri ya gamu, na ba shi ’yan rakiya ya tashi, ni kuma na koma Dara.
GWAMNATI TA KI SHAWARA, TA YI KUKA
Bayan Mahadi ya ci Lubayya, bai yi sakaci ba, sai ya mayad da hankalinsa wajen kara wa kansa karfi. Amma ba da bindiga da harsashi ya ke karawa ba, da harshe ya ke jawo mutane suna taruwa gare shi. Ya sami labari gwamnati tana gawurtaccen shirin yaki da shi, tana ta diban soja a Masar, kuma za a danka yakin a hannun Turawa ne gwanaye. Sabo da haka shi kuma sai aikawa ya ke ko ina cikin kasa, ana gaya wa mutane, cewa su shirya yin jihadi na sosai. Duk abin da aka yi da ba’a ce, murtuku na zuwa nan gaba. Ko wane gari sai shela a ke yi, ana gaya wa mutane su fid da zuciyarsu daga rayuwa a wannan duniya, gidan karya, ga aljanna can tana jiransu kofa bude! Jin haka fa kasa duk ta barko, maza da mata da yara suka taru a Lubayya. Masu zuwa yaki suka zo da shiri, mata da yara kuwa ziyara ta kawo su. Kowa yana so ya ga Mahadi, ko ma ya ji muryarsa.
Muhammed Ahmed Mahadi ya san yadda zai yaudari mutane. A waje kam, da ganinsa ka ga na Allah. Daga suturar jikinsa zuwa dabi’unsa duka babu na fahari. Jabba ce rigarsa a kullum, sai wando iyaka kwauri, sai hula makawiyya a kansa, ya zagaya mata dan guntun rawani kamu biyar. In yana tsaye a gaban jama'a yana wa’azi, ya kan nuna iyakar tawali’u da tsoron Allah, da nuna rashin kula da nishadin kome na duniya. Amma in ka gan shi a gida, sai ka ce ba shi ba ne. Abinci zababben gaske shi ya ke ci, mata yara kyawawa, da su ya ke hira. Duk lokacin da aka kamo ’yam mata a wurin yaki, kyawawan sai ya sa a daka, munanan kuwa a tura su kicin.
Yanzu kasar da Mahadi ya ci ta yi yawa, sabo da haka har ya tsara yadda zai shirya mulkinta. Da farko dai ya kafa baitulmali, ya nada abokinsa, Ahmed Wad Sulaiman, ma’aji. A gare shi a ke kawo su zakka da humushin ganimar yaki, da su tarar da a ke wa barayi, da mashaya giya ko taba. Salama ba ta kafu ba tukuna balle a shiga sa haraji. Ma’aji dai sai wanda ya ga dama ya taimaka. Shari’a kuma aka danka ta a hannun Ahmed Wad Ali. Da ma alkali ne shi a kasata, ya gudu ya koma gun Mahadi. Amma shari’ar da aka sakam masa kadan ce, don Mahadi ya sani lalle sai ya gama da iko, kana zai sami tabbatad da mulkinsa. Sabo da haka ko littattafan shari’a ma na hanyar Maliki, kona su aka yi don kada mutanensa su yi wata gardama. Ba a bar kome ba sai Alkur’ani, ko shi ma ba a yarda a karanta tafsirinsa ba, sai dai nassi kurum.
Gwamnati kuwa tana ta turo soja suna taruwa a Kahartum. Amma ko da ya ke shiri bai gamu ba, duk da haka a kan yi irin dan harin nan na wasa makamai. A cikin haka ne ma har kwamandan gwamnati, Abdulkadir Pasha ya kwato Kawa da Sennar, daga hannun Mahadi. Amma kwace wadannan garuruwa ko kadan ba su bata hankalin Mahadi ba. Abdulkadir Pasha kuma bai yarda wannan nasara ta rude shi ba. Ya san sai an yi da gasken gaske kana za a iya cin karfin Mahadi. Ya shawarci gwamnatin Masar ba daya ba, ba biyu ba, cewa kada a cika garaje wajen fada wa Mahadi, don kuwa lalle yana da karfi. Da tun farko gwamnatin Masar ta bi shawarar Abdulkadir, da ma’amalar yakin Sudan ba ta cabe yadda ta yi ba. Ya shawarce ta kada a aika da yaki Kordofan, ya ce ya kamata mayakan da a ke aikowa daga Alkahira sai a ajiye su a wurare wadanda su ke makarfafa a bakin Kogin Farin Nil. Mahadi kuwa a kyale shi a yanzu, sai karfimmu ya hadu sosai. Ko da wannan shawara ta kai Alkahira, sai aka murtsuke takardar kurum aka jefa a kwandon shara, aka ce zancen banza ne, a yi ta tura soja Kordofan. Aka danka wannan yaki a hannun wani janar Bature, wai shi Janar Hicks. Abdulkadir Pasha kuwa sai aka kira shi a Alkahira aka tube shi, aka danka kasar Kahartum a hannun Ala ed Din Pasha, wanda ke gwamnan kasashen Sudan na gabas. Duk wannan shiri kuwa yana kunnen Mahadi.
Da isowar Hicks Kahartum ya fara gwabzawa da Mahadawa a Marabia, ran 29 ga Afril, 1883. Aka hada shi da wani kwamanda wanda ke tsare da Duem, aka ce ya raka shi tare da nasa rundunar. Haka suka dunguma, ashe bakin ciki ke kiransu!
Lalle gwamnati ta yi kasaitaccen kuskure da ta raina karfin Mahadi. An yi zaton wadannan manyan rundunoni biyu za su iya watsa shirinsa. Am manta duk yammacin Sudan a hannunsa ta ke, am manta ya sami makamai masu yawa, kuma a cikin masu binsa da yawa sojojin gwamnati ne a da, suka koma bayansa. Am manta da karin maganar mutanen Sudan da su kan ce. ”Wanda ya auri uwata, shi ne ubana.” Tun da Mahadi ya ci su, yanzu shi suka sani, ba gwamnatin Masar ba.
Babban kuskure na farko, shi ne wajen shirya rundunan nan, da zabam mata hanyar da za ta bi. Soja dubu goma, da rakuma dubu shida, lalle suna bukatar tsarin tafiya mai kyau da kuma guzuri isasshe, ko da na ruwa. Amma ba a ce su bi ta hanyar da ruwa ya ke ba, ko da ya ke da damina ne. Sai aka kimsa su ta daji kurum, ga ciyawa duk ta shanye su, ba su iya ganin yadi dari a gabansu. Haka suka dinga tafiya yamamama kamar dango, sai kan rakuma a ke gani can kamar wani tsauni ke motsi. Rakumi dubu shida ne fa! Ana cikin tafiya, wani lokaci sai a hangi Mahadawa. A debi soja su bi su, wani lokaci a kore su, wani lokaci su koro. Haka aka dinga tafiya babu mai ratsewa, gudun karo da abokan gaba. Ko rakuma ma babu damar a kai su kiwo, sai dai su ci ’yar ciyawa da ke tsakiyar sahun soja. Wannan karancin abinci ya sa sun yi ta mutuwa kwarai. Abu dai ya kai matuka, yunwa ta shigam ma rundunar, da soja da rakuma kowa ya kasa. Wuya ta yi wuya har sojan ma suka fid da kuzarin yaki daga zukatansu, suka gwammace da ma Mahadawa su zo su kashe su, su huta da wannan wahala.
Muhammed Ahmed Mahadi kuwa da jin labarin runduna ta motsa, sai ya aika gari gari ana ta shela cewa kowa ya yi kalmar shahada, ya daura niyyar jihadi. Mutane ko ina sai gyaran makamai su ke yi, ana ta damara. Sai ya fito da runduna tasa daga cikin Lubayya ya zauna a karkashin wata itaciya ta kofar gari, yana jiran Misirawa. Nan wurin ya zama sansani, nan ne kuma kamar daffo, don a nan aka yi ta koya wa mutane dabaru iri iri na yaki, da hikimomin amfani da makamai.
Bayan rundunar Masar ta kusa Rahad. sai wani kalasaje, Bajamushe, ana kiransa Gustav Klootz ya goce, ya fita daga sahu, ya yanki daji ya nufi wurin Mahadi. Dalili kuwa don ya tabbata wannan runduna halaka za ta yi. Ya rage Lubayya da tafiyar kwana uku, sai ya gamu da wadansu baraden Mahadawa. Suka hau masa da duka, suka washe shi kaf, sa’an nan suka aiko da shi gun Mahadi. Da ya zo, sansani ya yi caa a kansa. Aka kai shi gaban Mahadi ya shiga masa tambayoyi game da halin da rundunar gwamnati ke ciki. Gustav ya fada masa sirrin kome, ya ce yunwa da gajiya sun ragargaza soja. Ya ce ko da ya ke Janar Hicks, kwamandan rundunar, ya yi alkawari ba zai nemi salama da Mahadi ba, sai am buga, amma bugawar ke da wuya za a ci shi. Jin haka Mahadi ya yi murna, ya sa wa Gustav albarka, ya shigad da shi Musulunci, aka ba shi doki da bindiga, ya zama cikin barade. Mahadi ya yi ta aika wa Hicks, ya ce ya kamata ya bi, don in sun buga abin ba zai yi masa dadi ba. Hicks ko sau daya bai taba ba da amsa ba.
Kafin Hicks ya taso daga Masar gwamnati ta yi masa alkawarin za a karo masa mutum dubu shida, amma har yanzu ko mutum guda bai zo ba. Mahadi kuwa kullum sai dura wa jahilan mabiyansa romon baka ya ke ta yi. Ran 1 ga Nuwamba ya bar Lubayya ya nufi Birket don ya tari Misirawa. Ran 3 ga wata, ran nan ya debi mutane ya ba wani kwamandansa wai shi Abu Anga, ya ce ya tari Misirawa a buga. Aka buga, mummunan bugawa. Kafin dai gari ya waye gawa ba ta kidayuwa!
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada

Post a Comment (0)