ABDULKADIR SALADIN 12

12. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Kafin Hicks ya taso daga Masar gwamnati ta yi masa alkawarin za a karo masa mutum dubu shida, amma har yanzu ko mutum guda bai zo ba. Mahadi kuwa kullum sai dura wa jahilan mabiyansa romon baka ya ke ta yi. Ran 1 ga Nuwamba ya bar Lubayya ya nufi Birket don ya tari Misirawa. Ran 3 ga wata, ran nan ya debi mutane ya ba wani kwamandansa wai shi Abu Anga, ya ce ya tari Misirawa a buga. Aka buga, mummunan bugawa. Kafin dai gari ya waye gawa ba ta kidayuwa!
Kashegari ran 4 ga Nuwamba, Hicks ya tura runduna gaba. Nan sansani kuwa daga tsibin gawa sai masu raunin da ba su iya tafiya. Runduna tana cikin tafiya, ba a ankara ba sai ga Mahadawa wajen dubu dari, suka yi kabbara a kan Misirawa. Nan da nan wuri ya harmutse, kafin dan lokaci kadan dai aka yi ta aka kare. Ban da hafsoshi Turawa da Turkawa, babu wanda ya ko dan tagaza. Kowa sai ya saki bindiga a harbe shi ya fadi. Ko su Turawan ma da Turkawan, nan da nan ko daya ba a bari ba, aka kashe su duka. Aka sa takobi aka cire kan wani janar wai shi Baron Seckeridorif da na Janar Hicks aka tsire a sandar mashi aka kai wa Mahadi. Shi kuma ya kira Gustav, Bajamushen da ya kawo kansa, don ya fadi sunayensu.
Ko wannensu yana da dogon gemu har da rerun wuya. Gustav ya ce Wane da Wane ke nan, ya nuna ko wane kai, ya fadi sunansa. Mahadawa suka komo Birket suna ta nashadin wannan nasara. Aka bar ’yan mutane kadan a fagen fama don su kwaso ganima su kawo baitulmali. Suka kwaso duk abin da ke wurin, hatta tufafin sojan nan dubbai da suka mutu, sun tubo, suka bar gawawakin huntaye. Ungulai da maiki da kura, kakarsu ta yanke saka, nama ya samu!
Bayan ’yan kwaso ganima sun komo, Mahadi ya shirya tashi ya koma Lubayya. Kai, babu abin da ya fi shigar wannan mutum Lubayya kwarjini. Yana gaba, sai tuta ke tashi, mutanen nan dubbai, barade da dakaru, duk suna dafe da bayansa, da haka ya shiga. Yanzu kuma babu wata shakka, cewa kulliyar Sudan a hannunsa ta ke. Daga Kogin Nil har Bahar Maliya, daga Kordofan har iyakar kasar Wadai, babu wani mai iko, mai fada a ji, sai shi. Wadanda tun farko suka yarda da manzancinsa yanzu sai kara Karfafa jama’a su ke yi. Wadanda kuwa ke shakkar gaskiyarsa a da, yanzu sun daina shakka. ’Yan kadan wadanda faufau har yanzu a wurinsu shi makaryaci ne, suka danne zuciyarsu suka bi, don su sami zama lafiya. Kasa dai dungum ta bi. Ganin haka, Turawa da Misirawa ’yan ciniki kowa sai daure kayansa ya ke yi, suka bar Sudan, suka fada Masar. Sun san Sudan dai yanzu ta Mahadi ce, ta ko fi karfin zamansu.
NA GA MAHADI
Bayan an hallaka rundunar Hicks Pasha, sai gwamnatin Masar ta hada kai da gwamnatin Ingila, bisa shawarar yadda za su yi maganin Mahadi. Aka ga babu wanda ya san kasar Sudan sosai da sosai a cikin sojan Masar, kamar Janar Gordon. Da gwamnatin Masar, da gwamnatin Ingila, da shi Gordon kansa, ba su san ainihin karfin Mahadi a Sudan ba. Duk sai bara da ka kurum su ke. Sun san yana da mayaka, amma a zatonsu ba shi da kayan fada irin na zamani, daga baka sai mashi. Mancewa suka yi ko da ya ke Gordon ya saba da Sudan, ya san mutanenta, kuma ya yi musu taimako iri iri na alheri, amma duk wannan bai sa su goce wa hanyar addininsu, su bi shi ba. Aka dai yi wa Gordon shiri sosai, ya taso daga Masar ya iso Kahartum ran 18 ga Fabrairu, 1884. Abin mamaki, mutane duk suka karbe shi hannu bude, saraki da jama’ar gari.
Da saukar Gordon Kahartum, abin da ya fara yi shi ne ya sa aka yi shela, cewa gwamnatin Masar ta nada Muhammed Ahmed Mahadi ya zama Suldanul Muslimina a Kordofan. An kuma yarda a koma ga cinikin bayi, kuma za su yi sulhu da Mahadi. A takardarsa da ya aika wa Mahadi da wannan sharadi,ya ce a saki duk fursunan yaki da aka kama, ya kuma hada da gaisuwar tufafi kyawawa. Kafin wannan takarda ta isa gun Mahadi, an riga am ba shi labari cewa Gordon bai zo da soja ba, sai 'yan kwarbansa kurum. Jin haka da isar takardar Gordon, Mahadi ya ce bai gane cewa am ba Shi abin da ya rigaya ya kwata da karfin kansa ba. Maganar nada shi sarkin Kordofan, wannan ai ruwan kwando ne, tun da ya riga ya ci kasar, kuma yana mulkinta. Sai ya shirya wa Gordon amsa, a ciki ya ce shi ba ya son surutan kawai. Abin da ya shawarci Gordon shi ne ya bi kurum, ya tsira da ransa!
To, mai karatu tambaye ni mana. Ni Slatin wane hali na ke ciki ne a kasata ? Na sani dai al’amari duka ya cude, tun da aka ci babbar rundunar da Janar Hicks Pasha ya zo da ita. Sabo da haka na fauwala al’amarina duka a hannun Ubangiji, shi ne kadai mai fisshe ni daga Sudan kuma. Yau kusan shekara ke nan ban sami wata wasika daga Kahartum ba ma, balle daga Masar. Da ni da sojana dai kamar an yashe mu.
Ran nan ina zaune ina tunanin irin wannan, sai ga manzo daga Zogal, wannan da na aika rahoton Mahadi. Ya aiko wani munafuki wai shi Khalid Wad Imam da labarun karya, cewa Mahadi karfinsa duk bai kai yadda a ke zato ba. In gwamnati ta turo runduna mai karfi, cinye shi za a yi. Ashe duk makirci ne. Zogal ya zama babban mutum a mulkin Mahadi, har an nada shi gwamnan yammacin Sudan. Ya turo Khalid don ya kwashe iyalinsa ne a boye, wadanda ke rike a hannuna, ya kai su wurinsa. Da na gane, na buge Khalid na daure cikin sarka na jefa shi kurkuku. Iyalin Zogal kuma duk na ce a kama su a tsare, na kwashe dukiyarsa na zuba baitulmali.
Na zauna cikin wannan hali, ba ni da labarin ko ina duk duniya. Ba ikon in aika da takarda Kahartum, ko a aiko mini, Mahadawa sai su tsare manzannin, su bubbuge su, su kwace. Ga shi ba ni da koshin makamai, ko harsashi ma sai goma sha biyu-biyu kadai ke hannun soja. Ko daya babu a taska. Kai, ran nan dai na ga babu abin yi sai in nuna wa mutanena, zan mika kaina gun Mahadi mu huta. Sun fi son haka, don sun gaji da yaki, kuma sun san ba mu da karfin karawa da Mahadi. Amma duk giri na ke musu, don dai kada su yi mini tawaye har kafin kila mu sami gudummawa. Na tashi manzo sai gun Mahadi da wannan sako. Muna cikin irin wannan zama, sai ga labari cewa ga Zogal nan da runduna tasa ya shigo Om Shanga.
Ran 20 ga Disamba, 1883, manzo ya komo daga gun Mahadi. Shi ya fada mini gaskiyar duk irin abin da ke akwai, da karfin Mahadi, da halakar Hicks Pasha. Ya zaro wasika daga Zogal ya mika mini. Ko da na buda sai ga Zogal yana cewa, ya kamata im bi kurum. Taurin kai ba zai fisshe ni ba. Baki ya boka, a maraicen ran nan sai ga manyan hafsoshin rundunata, su Farag Effendi, da Ali Effendi Tobgi, suka zo suka ce, da su da kulliyar soja sun yarda su daga wa Mahadi farar tuta. Da na tambaye su dalilin wannan abu, sai suka ce wai tun daga manjo har zuwa farabiti, duk sun tabbata ba mu da karfin taryar Mahadi. Bayan wannan kuma soja sun firgita da yaki, sun gaji da shi. Harsashi kuma ya kare karkaf. Suka ce su kam ba za su sake daukar bindiga don su yi yaki ba kuma!
Na ce su koma sai na yi shawara. Na shiga daki na kwanta. Ban iya barci ba a ran nan. Na dubi duk irin jidalin da na yi da wannan Shaidan, yau shekara hudu, da bakar wahalar da na sha, duk ya zama a banza. Yau ga shi ni da kaina zan je in durkusa a gaban Mahadi, in ce masa na bi shi. Na yi ta saka a zuciyata cikin dare, amma na rasa mafita ga wannan al’amari. Na dai sha gaya musu tun bara, cewa gudummawa na zuwa daga Kahartum, ga shi har yau ko labari. Na kuma sha gaya musu cewa ko ba dade, gwamnati ce za ta yi nasara. Ina cikin rike da su ta wannan karyar ke nan, sai ga labarin halakar rundunar Hicks Pasha. Jin haka ga shi sun ture. Mene abin yi ban da in nemi sulhu da Mahadi ? Kuma kowa ya san neman sulhu ba sauki gare shi ba, don sau da yawa shugaba shi kan fi shan wuya a hannun abokin gaba. Na kuwa tabbata wahala tana jirana a hannun Mahadi, tumbana da na ke Bature, kuma Kirista. Ko da ya ke na ce na musulunta, ina sallar karya, ina zikiri, amma a karkashin zuciyata na tabbata ni ba Musulmi ba ne. Kuma da yawa cikin mutanena sun tabbata musuluntana biri-boko ne.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
BBM: D61EAFAE
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada


Post a Comment (0)