TUN KAFIN AURE💐 10
Jikinsa har tsuma yake bai taba ganin macen da ta sace masa zuciya ba kamar wannan. Fatansa daya wannan saurayin daya rungumeta ba mijinta bane. Tura hotunan yariyar yayi daya gani a wayar ya tashi da sauri ya je wurin da Imi da Simy suke ta rawa yana mata liki da dubu daya. Janyo hannunta yayi suka fito daga wurin rawar Imi ya jawo wata suka cigaba. A irin wannan rayuwar ana tafka kazanta da tsabar rashin kishi. Muna mantawa akwai ranar da zamuyi accounting for every second da muka rayu a duniya.
Rawar ta cigaba da yi a gabansa ganin hakan ya sake janta suka kara nisa da mutane. Yarinyar nan nake son duk wani information a kanta. Ta dan nutsu ta kara kallon hoton wai wannan kake nufi? Eh mana are you blind? No...sai tayi dariya sorry. Gaskiya Juni bansan....katse mata magana yayi kada kice baki santa ba. Kudi ya dumbuzo daga aljihunsa ya damka mata a hannu. Ki nemo min duk abinda ya dace ...ya sake kallon hoton...my God she is so pretty. Kallonsa tayi Juni wannan fa pre-wedding pictures ne. Maybe ma anyi auren don na kusa wata da ganinsu. A wani group aka saka na ma manta wadda tayi sending. Ai sai ki sake sending ki tambaya. Look Simy bani account number dinki. Washe baki tayi yanzu kayi magana. Zan nemo ta ko tana gidan miji ne sai tazo ta kashe maka kishi...kanne masa ido tayi ta tafi. Simy 'yar shekaru goma sha tara karamar yarinya ce da iyayenta suka kyaleta take irin rayuwar da take so saboda yanayin aikinsu. Tana abinda taga dama babu me tsawatar mata a cewar su kuruciya ce ke damunta. Wai kuma yar musulmi kenan babu ko tsoron mutuwa.
******************
Kallon 'yan uwanta take ana ta hayaniya. Kanta har wani sarawa yake don ciwo. Wai nan lefenta aka kawo shine har yanzu mutane basu gama tafiya ba. Dakinsu ta nufa kai tsaye wata kakarta tace ai tunda kika dawo bamu watse ba ki tsaya ki kalli abin arziki. Ai ni kam wannan miji yayi ina ma ina da sauran kuruciya. Dariya duk aka sa Hafsi ko sai hawaye. Auren da zaayi ba dadin rai. Abinda komai Baban Saif ne yayi don yace shi ba karamin mutum bane aure ya zama dole. Shi kuma Saif kamar bai taba cewa yana sonta ba alaqar tasu yanzu ba yabo ba fallasa. Da gaske yayi nadamar abinda ya aikata sai dai kunyar iyalin Baffa yasa har ransa baya son ayi auren. Allah Yaso shaidan baici galaba a kansu ba da da wane ido zai tsaya a gaban mahaliccinsa? Ko matasa nawa ne ke tuna irin wannan a lokacin da suke matse 'ya'yan mutane suna aikata haramun?
Ita kanta Hafsi tana tsoron rayuwar da zasuyi. Da wane ido zasu rinka kallon juna. Ba don zuwan Baffa ba da kila shikenan. Rayuwa kenan wasu na nadama wasu kuwa zuciya ta gama bushewa a aikin sabo. Tir da wannan rayuwa ta shaye shaye da zinace zinace. Ya Allah Ka kara shiryamu Ka bamu wadatar zuci.
Batul Mamman💖