✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴
*ABOKIN FIRA *
*Rubutawa:* _Dr. Muhammad Mansur Sokoto_
*DRS NA 007*
*Bayan Wuya Sai Dadi*
A babban birnin Bagadaza ne, kuma a shekara ta 508 wata
irin fatara da halin kunci suka kama wani bawan Allah ana ce da shi Ahmad Ibnu Miskin. Ya ba da labarin cewa, a wannan shekara
sai da ya sanya gidansa da yake cikin sa tare da iyalinsa a kasuwa don neman samun sa’ida.
Ana haka watarana ya fita daga gidansa ko karin kumallo bai samu yi ba domin ba a tashi da komai ba, ban da ruwan sha a
gidan. Da ya hadu da wani abokinsa sai ya koka masa irin halin da yake ciki. Aka yi sa’a ya dauko fallen gurasa guda biyu an shimfida Zuma da Madara a tsakanin su ya mika masa, ya ce, ka je ka karya kumallo da wannan. Gogan naka sai ya ga ba zai iya cin wannan kayan dadi alhali ga ‘ya’yansa can suna jan ciki saboda yunwa ba. Don haka sai ya juya zuwa gida yana cike da
murna.
Bai yi nisa ba sai ga wata baiwar Allah dauke da yaro ta tsayar da shi. Ta ce masa, ya kai wannan bawan Allah, ka dubi Allah ka taimake ni. Wallahi ba ni da kowa a duniya sai Allah.
Mijina ya rasu, kuma wannan yaron da ka gan shi maraya ne, yana jin yunwa. Ahmad ya daga kai ya kalle ta sai ya ga idanun yaron ba abin da suke kallo sai gurasarsa. Sai da ya yi niyyar ya
sadaukar ya ba ta gurasar nan sai kuma ya tuna nasa ‘ya’ya. Ya rinka batun zucci, ya kulla wannan sai kuma ya warware. Kamar
daga sama sai ya ji zuciyarsa na cewa, ka ba ta, Allah zai saka maka. Da ya miqa mata gurasar sai ta fashe da kuka saboda murna da jin dadi. Shi kuma ya juya damuwa ta lullube shi ta ko ina.
A kan hanyarsa kuma sai ya gamu da wani mutum dan
unguwarsu sai yake ce masa, kana ina ne tun dazu ga baki can kofar gidanka suna neman ka? Ni?! Ahmad ya fada cikin tashin
hankali. Ya ce, eh. Ga wasu mutane can daga birnin Dimashqa
suna neman ka. A nan fa Ahmad ya sake shiga wani tashin hankali. Domin kuwa da me zai tarbi wadannan baqi shi da yake ko Garin Kwaki bai aje a gida ba! Ya yi ta sake sake a cikin zuciyarsa, kamar ba zai je gidan ba. Amma ya daure ya isa. Da ya zo ya tarar da wani dattijo kamili a qofar gidansa tare da wasu matasa sun jawo masa jerin raquma iyakar ganin ka Da suka gaisa, dattijon ya tambaye shi labarin mahaifinsa
Al-Miskin, sai ya ce ai ya cika tun sama da shekaru talatin. Dattijo ya jajanta masa sannan ya fada masa dangantakar da take
tsakanin su. Ya ce, ai ni babban amininsa ne. na san ka tun kana yaro karami sosai. Sannan ya labarta masa yadda ya karbi rancen
kudi daga hannun mahaifin nasa amma da sharadin zai yi kasuwanci su raba riba. Ya ce, a cikin ikon Allah sai kudin duk suka salwanta. Jin kunyar mahaifinka ya sa na bar garin nan zuwa birnin Dimashqa. Kuma tun da na tafi Allah ya yi mani budi na
samu arziki da wadata daidai gwargwado. Ya ce, tun a lokacin na ware masa kudinsa na sa ake juya su. Duk abin da ka gani a nan
raqumansa ne kuma ma ga sauran canji a hannuna. Ya kawo wasu maqudan kudi ya hannunta masa. Da aka wayi gari ya juya ya kama hanyar komawa gida ko tukuici bai karba ba.
Ibnu Miskin ya ci gaba da ba da labarin cewa, ya dauki duk wani mataki na godiyar Allah bisa wannan ni’ima. Da farko dai ya nemi wanda ya ba shi gurasar nan ya saka masa. Sannan ya nemo wannan baiwar Allah ita da marayanta ya kyautata masu.
Kai, duk da wanda ya ba shi labarin zuwan bakin nan sai da ya yi masa kyauta mai mantar da talauci. Sannan ya ci gaba da kasuwanci yana juya kudinsa kuma yana yawan alheri. Har ta kai
ma duk wani aikin taimako ba ya da wata madogara in ba shi ba.
Ana cikin haka ne sai Shaidan ya so ya samu sa’ar sa. Ya fara nuna masa cewa, ai ladarsa ta yi yawa a yanzu. Watakila ma takardun aikinsa sun cika da lada ba sauran wurin da ya rage da
za a ci gaba da rubutawa. Da Allah ya so shi da rahama sai watarana ya kwanta ya yi mafarki. Aka nuna masa an yi tashin Alqiyama. Sai ya ga ana ta auna ayyukan mutane, kowa yana dauko nasa yana kawowa ana auna masa. Da aka zo kan sa sai aka ce ya fara dora zunubinsa a kan sikeli, sannan aka ce ya dora
ladarsa. Da farko ladarsa ta rinjayi zunubinsa. Amma sai wani Mala’ika ya zo yana qara binciken kayan ladarsa. Ya riqa fitar da wasu ababe baqi kirin kamar ‘yan kananan duwatsu masu dan
karen nauyi yana cewa, ban da wannan, a cire shi, Riya ce. Har sai da ladarsa ta koma kamar auduga ba nauyi, kamar iska zai
dauke ta. Don haka bangaren zunubi ya rinjaya. Sai ya fashe da kuka. Can sai ga wani Mala’ika ya zo yana cewa, a saurara!
Wannan bawan Allah yana da wani aikin alheri da Allah ya ba mu ajiyar sa. Sai ya fito da gurasa guda biyu ya dora masa a kan aikinsa. Nan take sai sikelin ya danqara ya yi qasa amma bai iya
rinjayar zunubin ba. Sai wani kuma ya taso ya ce, akwai abu daya da ya rage masa wanda ba a zo da shi ba, ku dakata in dauko. Sai
ya zo da wata ‘yar qaramar kwalba ya fito da ita ya riqa diga ruwan da ke ciki a kan kayan lada. Ya ce, wannan hawayen matar nan ne na farin ciki da ka sanya ta. Yana cikin digawa sai sikelinsa na dama ya rinjaya. Mala’iku suka ce, Ma sha Allah! Yanzu kam ya
tsira. A nan ne ya zabura ya farka daga barci.
*Darussa:*
▶ Kada ka taba yanke qauna daga rahamar Allah. Bayan wuya sai
dadi.
▶ Idan ka samu ni’ima ka fara tuna iyalanka.
▶ Har abada na-Allah ba su qarewa
▶ Ka riqe Amana sai Allah ya taimake ka.
▶ Wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi.
▶ Idan ka ci bashi da nufin biya Allah zai biya maka.
▶ Idan Allah ya yi maka ni’ima ka gode masa.
▶ Ka yi alheri. Ko ba ka ci moriyarsa ba ‘ya’yanka za su ci a bayanka.
▶ Komai za ka yi ka yi don Allah. Amma fa kada ka rudu da yawan aikinka.
▶ Karamin aiki da kyakkyawar niyya ya fi babban aiki da aka yi shi
bisa riya.
▶ Hattara da tarkon Shaidan.
▶ Idan Allah ya so ka, ko a mafarki sai ya yi maka ishara.
▶ Nuni ya ishi mai hankali.
▶ Sadakar abinci ta fi komai amfani ranar Alqiyama.
📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕📕
Email: jibwissocialmediaktlg@gmail.com
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 08034453678, 08036958490.