Tun KAFIN AURE 33

TUN KAFIN AURE💐 33



Tana kwance suna hira cikin nishadi nurse din ta dawo. To angama komai ina kudina? Rosie ta dauko dubu ashirin a jakar Tilly ta mika mata. Ki dai tabbatar babu wani cikin wadanda suka kawo mu babu wanda ya shigo. Nurse Talle ta washe baki tana murna ta ce angama ranki ya dade. Bata dade da fita ba Dr Sunusi ya shigo dakin tare da wata nurse din. File ya bude yana dubawa, ya dan dago kai kece Talatu Jibo ko? Eh ta amsa da kyar tana ta rike ciki ita a dole mara lafiya. Yanzu likita na rasa baby na kenan? Kiyi hakuri mana ki dena kukan Rosie ta fada tana rarrashinta. Dr yace ya naga kina rike ciki ne ko bai gama fita bane? Saurin sakin cikin tayi ya fita duka ni dai ku sallameni kawai na tafi. Ya kalli nurse din kinga ki gyara min dakin can zanyi mata wankin ciki, ya maida kallonsa ga su Tilly. Ai kada ki damu idan nayi miki wankin cikin before you know it zaki sami wani. Yadda kike rike cikin nasan akwai saura. Wannan karon kukan gaske ta saka masa kayiwa Allah likita kada kayi min wallahi cikin baya ciwo ko kadan. Yace ai dalilin wankin kenan idan akayi bari ba ciwo nan ma akwai serious problem. Tana kuka yace a kawo wheelchair a kaita dakin da zai mata a can.
Kankame Rosie tayi bazata tafi ba. Rosie tace kiyi hakuri Tilly kada asirinmu ya tuno. Saboda tsabar  kwadayin daya kawo su Tilly tana ji tana gani akayi mata D and C. Likita dai yasha zagi ta uwa ta uba.

Sai dare aka sallamosu duka a gidan suka hadu da Hamida suna jiransu da Senator. Ko daki basu shiga ba Rosie tace yallabai munyi waya da kawu na baban Talatu yace gobe zaizo gari don na fada masa abinda ya faru. Anyi mata fyade kuma anyi sanadin zubar da cikin. Wallahi maganar nan har yan jarida sai na fadawa. Kowa kallonta kawai yake tana rashin kunya Senator ya hanasu magana a cewarsa dansa ne ya ja masa. Tana gamawa yace idan sunzo goben zaa daura musu aure da Junaid. Yana gama magana ya juya zai haye  sama zuciyarsa na kona saboda bacin rai. Ta sake cewa ita kuma wadda ta zubar da cikin idan zaayi adalci sai a saketa ko a dau mataki. Hamida tace uban kuturu kuma yayi kadan in fada miki. Hafsi mutu ka raba da Junaid. Hajiya tace ku wuce ku tafi gidajenku Allah Ya bamu alkhairi.

Junaid da Hafsi basu san abinda ke faruwa ba saboda ya wuce  pharmacy da ita neman wani magani. Ac ya ware mata ya ja mayafinta can baya yadda cikin zaisha iska. Motar ko radio bai kunna ba yana ta kallon yadda Hafsi take ta zumbure zumbure. Yasan itama laifinsa take gani ya jawo musu masifa har gida an rasa yadda zaayi dasu saboda gudun abinda zaije ya dawo tunda babansa dan siyasa ne. Tarkace da yawa ya siyo mata na kwadayi bayan ya siyo maganin. Ganin bata da niyar kula shi yace Hafsi Hafsi kiyi hakuri akan abinda ya faru. Bansan dalilinta nayi miki sharri ba amma zanyi maganin abin. Tsautsayi ne ya kaini ga saninta amma kisa a ranki wallahi bazan aureta ba don nasan ko wacece Tilly. Cikin takaici yake maganar Hafsi tayi biris dashi. Ba komai ke damunta ba face yadda aka kasa gano karyarsu kuma ita bata da wani shaida akan abinda taji. Tasan Nafisa ta yarda da ita amma idan basuyi wani abun ba suna kallo Senator zai sa Junaid ya auri wannan matar. Wai ma ya akayi suka yarda bari tayi ne? Ko dai da cikin gasken? Ita ta gama zama confused. Har ta fara kokonto akan abinda kunnenta ya jiye mata




Batul Mamman💖

Post a Comment (0)