LABARI MAI TA6A ZUCIYA.
Na karanta wannan labarin ne a wani shafi a internet...wanda ya sakani Hawaye....
Mahaifiyata ta kasance mai Ido Daya. Wannan yasa a duniya babu wadda na tsana kamarta, domin a lokacin Mahaifiyata ita ke dafawa Malamai da Daliban Makarantar mu Girki ta hakan take samun damar biya min kudin Makarantata, yan ajinmu sai suyita yimin dariya cewa Mahaifiyata ido Daya gareta, hakan ni kuma kesa nake qara tsanarta. Kusan kullum na kan zo na tsareta ina cewa "Mama wai me yasa a lokacin da kika rasa idonki daya baki mutu ba?" haka dai nake nuna mata tsana kiri kiri amman bata ta6a nuna min 6acin ranta ba. A haka dai har na samu na kamalla Secondry na, na samu certificat na koyarwa a Singafor, haka na tattara na koma can da zamana har na gina gida nayi aure acan na haifi yarana da Matata muna zaune lafiya cikin Farin ciki, amman ban qara tuna cewa wai inada wata Mahaifiya dana baro a gida ba. Kwatsam wata rana sai ga Mahaifiyata ta kawomin ziyara, koda ta qwanqwasa kofa Yarana suka bude, suna ganinta suka tsorata suna kyankyaminta. Koda nazo na tarar da ita Haushinta ya kamani nace da ita " Me yasa kika zo? Gashi yanzu kin tsorata min Yara.. Gayyatarki nayi? Dan Allah ki koma daga inda kika fito...!"
Cikin sanyin murya tacemin "Kayi hakuri 'Dana bansan haka zata faru ba..."
Koda ta gama fadar haka ta juya ta tafi, tafiyar da ban sake ganinta ba.
Bayan wasu shekaru, a primary dinda nayi, inda Mahaifiyata ke aiki, aka shirya wani taro na tsofin dalibai. Nayiwa Matata qarya akan zanyi tafiya ne zuwa wani gari.
Bayan naje an gama taron sai naji ina sonn zuwa tsohon gidan mu inda Mahaifiyata take, koda naje sai maqotanmu suka cemin ai mahifiyata ta dade da rasuwa amman ta barmin wata wasiqa. Ban wani damu ba da samun labarin mutuwarta.
Koda na bude wasiqar da tabarmin sai na karanta kamar haka :
"Ya kai Yarona,, ina kewarka a kowanne lokaci. Ina mai baka Hakuri akan zuwa da nayi Singafor na tayar maka da Hankali da iyalenka. Naji dadi sosai da zuwanka wannan taro da aka shirya, amman saidai a wannan lokacin bana raye, bare na ganka ka. Ina baka hakuri dana kasance kamar wata Dodo a cikin rayuwarka, ina fata zaka gafartamin?
A lokacin da kake yaro karami, kayi wani hatsari inda ka rasa idonka daya. A matsayina na Uwa bazan iya ganin ka girma da ido daya ba, hakan yasa naje asibiti aka cire tawa aka samaka. Naji dadi sosai Yarona ka girma kana gani radau ta inda har gashi yau da ka tara iyali, dan Allah idan ka koma gida ka shafamin kan Jikokina. Allah ya maka Albarka... MAHAIFIYARKA mai kaunarka a koda yaushe."
A lokacin da na karanta wannan labarin saida nayi kuka! Domin labari ne mai ta6a zuciya.
Uwa uwa ce a kowanne hali take...
INA SONKI MAHAIFIYATA FIYE DA KOMAI....
YA ALLAH KA JIKAN IYAYENMU KA SASU A CETON MANZAN ALLAH (SAW)...Ameen
Please share to groups...
Ku cigaba da ziyartar shafin domin samun Labarai masu Mahimmanci 👉🏽 Www.Ashblog.com.ng

Labari mai sa hawayi cikin tausayi.. Allah ya bamu ikon bin iyayenmu
ReplyDelete