BAYYANA ƁARNA YANA DAGA CIKIN MANYAN SABUBBAN JANYO BALA'I

BAYYANA BARNA YANA DAGA CIKIN MANYAN SABUBAN JANYO BALA'I

Alal hakika mai sabon Allah a boye, yana mai jin kunyar Allah, yana jin kunyar mutane, yana jin cewa; sabon Allah yake aikatawa saboda ya san haramun ne a Shari'a, -ta yiwu ma har in ya gama biyan bukatarsa zai yi Istigfari ya nemi tuba a wajen Allah-, ya fi saukin laifi a wajen Allah a kan wanda yake aikata sabo a bayyane, ba jin kunyar Allah ba jin kunyar bayinsa.

Lallai fa aiyukan sabon Allah mataki-mataki suke, gwargwadon barnarsu a cikin al'umma. Shi ya sa wanda yake da dadiro a boye sharrinsa ya fi sauki a kan wanda yake gaisawa da mata hanu da hanu a bainar jama'a. Mai boye aiyukan sabonsa ya fi saukin laifi a kan mai bayyana aiyukansa na sabo. Haka yin maganganun banza a boye ya fi saukin laifi a kan mai ba da labarin banza wa mutane a bayyane. Masu bayyana aiyukan sabo sun yi nisa da afuwar Allah Madaukaki. Annabi (saw) ya ce:
"كل أمتي معافى إلا المجاهرين، وإن من المجاهرة أن يعمل الرجل بالليل عملا، ثم يصبح وقد ستره الله عليه، فيقول: يا فلان، عملت البارحة كذا وكذا، وقد بات يستره ربه، ويصبح يكشف ستر الله عنه".
صحيح البخاري (8/ 20) صحيح مسلم (4/ 2291)

"Dukkan al'ummata za a musu afuwa sai dai masu bayyana laifuka, kuma daga cikin bayyanawan akwai, mutum ya aikata wani aiki (na laifi) da daddare, sa'annan ya wayi gari alhali Allah ya rufa masa asiri, sai yace: ya wane, jiya na aikata kaza da kaza, alhali ya kwana Ubangijinsa yana rufa masa asiri, sai ya wayi gari yana tona asirin da Allah ya rufa masa".

Shi ya sa Bilal bn Sa'ad ya ce:
"إن المعصية إذا خفيت لم تضر إلا صاحبها، وإذا أعلنت فلم تغير ضرت العامة".
شعب الإيمان (10/ 80)

"Shi aikin sabo idan aka boye shi to ba zai cutar da kowa ba sai mai shi kawai, amma idan aka bayyana shi, kuma ba a canza shi an yi inkari ba to zai cutar da dukkan al'umma".

Shi ya sa Allah ya ce:
{ وَاتَّقُوا فِتْنَةً لَا تُصِيبَنَّ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْكُمْ خَاصَّةً وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ } [الأنفال: 25]

"Ku kiyayi fitinar da ba za ta shafi masu laifi kawai ba, ku sani lallai Allah mai tsananin uquba ne".

Kuma a yau yana daga cikin bayyana aiyukan sabo mutane su je su hole a shagalin bikukuwa a kebance sai kuma a zo ana ta yada hotuna da faifan video, sai ya zama kamar a gaban jama'a a ka yi ba a wani waje kebantacce ba.

Saboda haka abin da muke gani na munanan shagalin bikukuwa da Musulmai suke yi a wannan zamani ya yi munin da zai iya janyo mana fushin Allah da bala'i da azaba gama gari.

Saboda haka wajibi ne mu nisanci aiyukan sabo a boye balle kuma a bayyane.

Mal. Aliyu Muh'd Sani

Post a Comment (0)