Tambaya
:
Mene ne hukunci akan matar auren da taje tayi zina, shin auren ta yana nan ko kuma ya lalace? Sannan kuma dole ne sai tayi Istibrā'i kafin mijinta ya sake saduwa da ita ko kuma a'a?
:
Amsa:
:
Hakika laifi ne babba ga musulmi yaje ya aikata zina, Shin ya na da da aure ko ba shi da aure haramun ne a gare shi yayi zina, domin zina tana daga cikin manyan laifuka da Allah(ﷻ) ya haramta akan dukkan musulmi namiji ko mace, Kamar yadda Allah(ﷻ) yake cewa:
:
ولا تقروا الزني، إنه كان فاحشة وساء سبيلا، (سورة الإسراء/32)
MA'ANA:
Allah(ﷻ) yace: kada ku kusanci zina, domin ita alfahasha ce da kuma mummunar hanya:
:
Danhaka yazama wajibi a gareta ta tuba ga Allah(ﷻ) ingantaccen tuban da ba za ta sake aikata irin wannan danyen aikinba,
:
To amma dangane da maganar cewa ko aurensu yana nan ko baya nan zance mafi inganci shine auresu yana nan, haka nan magana mafi inganci daga cikin zan tukan da Malamai suka yi akan wannan matsala shine cewa mijinta zai iya ci gaba da saduwa da ita ba tare da ta yi wani Istibrā'i ba, duk da cewa akwai Malaman da su ka ce dole sai tayi Istibrā'i, daga cikin malaman wasu suka ce jini-3 za ta yi, wasu malaman kuma su ka ce jini-1 za ta yi, to amma magana mafi inganci babu wani Istibrā'i da za tayi, domin idan wani daga cikin ma'aurata yaje yayi zina, to wannan zinar ba za ta bata auren dake tsakaninsu ba, amma inda ace mace ba ta da aure ne to shi ne za tayi istibra'i, Sai dai abin da Malamai sukace shi ne idan Miji yasan cewa Matarsa mazinaciya ce to abu mafi kyau shine kawai ya rabu da ita, domin zata iya bata masa Zurriyya.
:
To amma idan matar aure taje tayi zina kuma sai ya kasance ciki ya shiga a sakamakon zinar da tayi, to ashari'an ce za a jingina wannan cikin ko kuma dan da ta haifa zuwa ga Mijin da ta ke aure amatsayin ubansa, saboda Manzon Allah(ﷺ) yace:
(الولد للفراش وللعاهر الحجر)
Sai dai idan shi Mijin ne ya kore yace ba dansa bane to shike nan sai ajingina shi zuwaga Mahaifiyar sa.
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/