DALILAN SHAN AZUMI GUDA GOMA SHA BIYU (12). BISMILLAH.
Sharia ta Amincewa masu larura susha azumi:
» Wasu zasu Rama.
» Wasu su ciyar.
» Wasu baza su ramaba, kuma bazasu ciyar ba.
GASU KAMAR HAKA:
1. Mara lafiya, zaisha azumi idan ya warke sai yarama.
2. Matafiyi, zaisha azumi saboda tafiya, saiya Rama daga baya.
3. Mace mai jinin al'ada zatasha azumi idan tayi tsarki, saita Rama.
4. Mai jinin haihuwa, idan jini yadauke sai tarama.
5. Mai ciki, wacce taji tsoron wani abu zai sameta, koya sami dan cikinta.
6. Mai shayarwa, wacce taji tsoron cutuwa gareta ko dan da take shayarwa.
7. Tsoho ko tsohuwa wadanda tsufa ya hanasu yin azumi, sai su ciyar kawai babu ramuwa akansu.
8. Mahaukaci, idan ya warke sai ya rama idan kuwa, babu waraka ya sauka akansa babu ramuwa babu ciyarwa.
9. Qaramin Yaro, azumi ba wajibi bane akansa, sai dan sabawa.
10. Mai farfadiya, idan farfadiya tazowa mutum yana azumi, bazai ramaba idan ya farfado.
11. Mai ciwon Qishirwa, wanda bazai iya azumi ba, sai ya dinga ciyarwa kawai.
12. Mai ciwon yinwa Ulcer (olsa) wanda, baya iya daukar lokaci mai tsawo sai yaci abinci, shima sai ya dinga ciyarwa.
SHARHI:
Mai ciki da mai shayarwa, suna matsayin marasa lafiya idan sun sami dama sai su Rama. Amma, wasu Malamai suna ganin idan ciyarwa ma sukayi yayi dai-dai.
WALLAHU A'ALAM.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
Allah ya datar damu bijahi sayyidis sadati SAW.
DAGA NAKU...
*HABIB YUSUF INDABAWA*