YADDA ZA KI SHIRYA ALALEN SHINKAFA


YADDA ZAKI SHIRYA ALALEN SHINKAFA

ABIN BUKATA

Shinkafa ta tuwo
Kwai
Nama
Hanta
Attaruhu
Albasa
Magi
Gishiri
Curry
Main gyada

Yadda Ake Yi:

A wanke shinkafa a shanya ta bushe akai a nukata a tankade a kwaba da ruwa kamar kullun alala a jajjaga attaruhu a zuba a yanka albasa a zuba a yanka dafaffiyar hanta kanana a zuba ki daka dafaffan namanki ki zuba,

Ki zuba dafaffan kwai da kika yanka, ki zuba magi da gishiri da curry kisa mai yadda zaiyi, ki jujjuya saiki zuba a leda ki dafa kamar alala, idan kuma na gwangwani zakiyi sai ki zuba mai a gwangwani jki zuba kullun ki turarashi, idan yayi sai a kwashe a zuba plas shikenan. 
Post a Comment (0)