SALLAN ASUBA MALA'IKUN DARE SUNA HALARTA DA MALA'IKUN RANA
🍃💦🍃
Daga Sahabi Abi Hurairah Allah (T) ya kara masa yarda.
Lalle Annabi S. A. W yace: "Suna yin karɓa-karɓa a cikin ku, waɗansu mala'ikun da dare waɗansu da rana, amma suna haɗuwa a Sallan Asuba da Salan Asri, sannan se su hau waɗanda suka kwana acikin ku, se (Allah Ta'ala) ya tambaye su, alhali ya fisu sani, ya kuka baro bayina, se suce: Ai mun baro su suna Sallah, kuma dama mun same su suna alhali suna Sallah.
.
-imam Bukhari da, Muslim (Dariqus-salihin)
# Zaurenfisabilillah
Telegram:https://t.me/Fisabilillaaah