TAMBAYA TA 028

*Tambaya:*


Assalamun Alaikum dafatar kana lfy Allah ytaimaka Dan Allah malam inadatambaya watace tayifada damijinta saiyacemata yaudinnan zaisaketa kuma zai aikomata datakardansaki harkuma ankwana biyu baikarayin maganarba kuma baibada takardanba Dan Allah yanxu yazatayine
.

*Amsa:*


Waalaiku mussalam.
 
Duk maganar da aka yi muddin ta tsaya a niyya ba a zartar ba, musamman maganar saki tunda ya ce ga lokacin da zai yi kuma har aka kai be tabbatar ba to ba wanda ze tabbatar masa, kuma ta iya yiwuwa gargadi ya yi don wani laifi a kiyaye.

Manzon Allah saw ya ce:
*”ان الله تجاوز عن أمتى فيما حدثت أنفسها,او ما تكلمت به,مالم يعملوه“.* الترمذ

*"Lallai Allah Yana yafe ma al'ummata abin da suka yi na zancen zuci ko maganar baka, muddun basu aikatashi ba.”* tirmizy 

Akwai abinda da zarar ka furta to ya zartu koda wasane kuwa, kamar saki, kyauta, ridda. Wannan ya aiyana lokaci, lokacin ya yi be tabbatar ba, to maslahar itace a tambaye shi maganar nan ta tabbata ne ko ko, in ta tabbata to se a nemi sheda.

والله اعلم.
.

*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*

*🕌Islamic Post WhatsApp.*

Post a Comment (0)