Tambaya
:
Mene ne hukuncin Sallar Mutumin da ya sara ruwan alwala sannan kuma ya rasa ƙasar da zai yi taimama da ita??
:
AMSA:
:
Malamai sun yi saɓani dangane da mutumin da bai samu ruwan da ze yi alwala ko wanka da shi ba, sannan kuma bai samu ƙasar da ze yi taimama da ita ba, dangane da wannan mas'ala an samu maganganun Malamai kamar guda(4) a kan haka:
:
1-Waɗansu Malaman sukace ba zai yi wannan sallah ba dole sai in ya samu ruwa ko kuma ƙasar da zai yi taimama da ita sannan yayi:
:
2-Waɗansu Malaman sukace ba zai yi wannan sallah ba kuma ba zai ramaba:
:
3-Waɗansu Malaman sukace ze yi sallar amma idan ya samu abin da ze yi tsarki da shi to wajibi ne sai ya ramata:
:
4-Waɗansu Malaman sukace wajibi ne yayi sallar a haka kuma babu wata ramuwa akansa da zai sake yi:
:
Danhaka Malaman da suka tafi akan wannan fahimta ta ƙarshe sukace, idan Mutum ya samu kansa a yanayin da babu ruwa kuma babu ƙasar da ze yi taimama da ita gashi kuma lokacin sallah yayi, to kawai ze yi sallarsa ne a haka ba tare da alwala ko taimama ba, kuma sallarsa ta cika ba sai ya sake wata ba ko da kuwa ya samu ruwa a cikin lokaci ko kuma bayan lokaci. Wadannan Malamai sun kafa hujjar su ne da faɗin Allαн(ﷻ) cewa:
:
"فاتقوا الله مااستطعتم"
MA'ANA:
Kuji tsoron Allαн(ﷻ) gwargwadon iyawarku:
:
Sannan kuma acikin wata ayar Allαн(ﷻ) ya ke cewa:
:
"لا يكلف الله نفسا إلا وسعا"
MA'ANA:
Allαн(ﷻ) ba ya kallafawa rai (ya ɗora mata aikin da yafi ƙarfinta) sai dai abin da (ita rai ɗin) za ta iya ɗauka:
:
Sannan lokacin da Mαnzon Allαн(ﷺ) ya umarci Sahabbai da suje su binciko abin wuyan Nana A'isha da ya ɓata, to da lokacin sallah ya yi sai sukayi sallarsu a haka saboda ba su da ruwan alwala, kuma a lokacin ba a saukar da hukuncin yin taimama ba, da sukazo suka yiwa Mαnzon Allαн(ﷺ) bayanin yadda sukayi bai ce da su su sake wata sallar ba, sai dai ma ya tabbatar da su ne a kan hakan, kuma a dalilin faruwar wannan abu Sai Allαн(ﷻ) ya saukar da ayar taimama:
:
Danhaka Malamai sukace wanda ya samu kansa a haka to babu abinda ya ke wajibi akansa sai dai yaji tsoron Allαн(ﷻ) gwargwadon iyawarsa, domin dukkan abinda Mutum ya kasa samun iko a kansa kamar wanda ya rasa tufafin da zai suturce jikinsa da shi, ko kuma yana da tufafin amma akwai najasa a tare da su kuma babu wasu tufafin da zai sa, to Shari'a ta yarda cewa ya yi Sallarsa a haka, domin hukuncin wajabcin waɗannan abubuwa duk sun faɗi akansa:
:
Danhaka dai maganar da tafi Inganci a cikin dukkan maganganun da Malamai sukayi kuma take da dalilai masu ƙarfi itace ƘAULIN da Malamai sukayi cewa wajibi ne Mutum ya yi Sallarsa a wannan halin da ya samu kansa aciki: kuma sallarsa ta cika a wajen Allαн(ﷻ): babu wata ramuwa da zai sake yi:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Daga Zaυren
Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/