Assalamualaikum
= TAMBAYA=
Ance mutuwar annoba shahada ce hakane mallam, sannan wani nau'in ciwo ne yake zama annoba? Jazakumullahu khair
=
AMSA
=
Wa'alaikumussalam warahamatullah wabarkatuhu
Na,am Al-imam Nawawi Rahimahullah acikin Littafin sa me Suna "Riyadus saliheen" ya bude babi me suna :-
235 - باب بيان جماعة منَ الشهداء في ثواب الآخرة ويغسلون ويُصَلَّى عليهم بخلاف القتيل في حرب الكفار
=
Acikin haka yakawo hadisai daga Bukhari da muslim dasuke tabbatar da Annoban data riski mutum harya mutu, tofa shahadace "matuqar ya mutu musulmi baya shirka!" sedai fa mu bazamu cemar wane Shahidi bane, sedai zamu iya cewa "wane yayi mutuwa irin mutuwan shahada, ALLAH ya kar6i shahadan sa" sa6anin 'yan shi'a ! Daga sun hadu da Buratai ! Sekaji sunce wane yayi Shahada !
=
Dan haka Dai "duk wani abu daza'a iya cemar annoba me cutar wa a garin ku, to sunan shi annoba a musulunchi in Sha ALLAH:- kaman gobara, ciwon amai da gudawa, lassa fever.... Da sauran su, mutuwa acikin ruwa...
=
Amma dai za'a musu wanka a musu sallah, sa6anin Wanda ya mutu a filin daga wajen yaqan kafurai! Shikan ba wanka ba sallah ba samar likka fani....
Wallahu a,alam
02-06-1441
28-01-2020
===============
*Domin samun Darrusan addini Cikin harshen Hausa...↓↓↓*
====================
» » » Facebook.com/khulafaurrashidun
» » » Whastapp
07035269582
09033206238
08063796175
» » » Telegram https://t.me/joinkhulafa
»»» Website
www.khulafau.cf
Youtube » https://youtu.be/jsUkIOaww3