Article 011//
ABUBUWAN DA BASA BATA AZUMI
Fitar haƙori ko zubar jini kamar habo na hanci da makamantan su to suma basa bata Azumi.
Fitowar Alfijir alhali Ƙwaryar abincin ka tana hannun ka, to kada ka ajiye, har sai ka gama biyan buƙatar ka, kuma Azumin ka yayi, ba ka da wani laifi akan haka; dalili akan haka fadar Manzon Allah ﷺ inda yace: “Idan ɗayan ku yaji Kiran Sallah, alhali Ƙwaryar cin abincin sa tana hannun sa, to kada ya ajiye wannan ƙwaryar, har sai ya kammala biyan buƙatar shi”.
[Abu Dawuda ne ya riwaito shi daga Abu Hurairah]
Duk wanda ya jinkirtar da yin wankan sa na Janaba da daddare har sai da Alfijir ya fito, to shima babu laifi akan shi, sai dai abunda yafi dacewa kayi gaggawar yin Wankan; saboda ka riski falalar Sallah a cikin Jam’i; dalili akan haka Nana Aishah Uwar Muminai (Allah ya ƙara mata yarda) tace: Lallai na shaida hakika Manzon Allah ﷺ yana kasance ya wayi gari yana mai Janaba ta Iyalin Sa bata mafarki ba kuma ya cigaba da Azumin Sa. [Bukhaariy ne ya riwaito shi]
Kenan, mai Haila ko mai Jinin Biki idan suka tsarkaka tun cikin Dare wato jinin su ya dauke to ya halasta gare su su jinkirta Wankan su har zuwa bayan bullowar Al-fijir.
Ƙaho: wasu daga cikin Malamai sun tafi akan cewa Ƙaho yana iya karya Azumi, suna masu kafa hujja da Hadisin da Annabi yace: “mai yin Ƙaho da wanda ake yima wa Kahon duka Azumin su ya karye”. Kuma babu makawa wajen ingancin wannan Hadisin, sai dai Malaman suyi bayani dalla-dalla akan haka, sukace; idan har anyi maka Kaho zai sa ka galabaita to anan ne Azumin ka ya karya, amma idan anyi maka baya kai ga galabaitar dakai to Azumin ka yana nan bai karye ba, saboda akwai Hadisin da yazo ya inganta daga Abdullahi dan Abbas – Allah ya kara mishi yarda – yace: Annabi (SAW) yayi Ƙaho alhali yana Azumi, kamar yadda Bukhaariy ya ruwaito a ingantaccen littafin shi, a takaice dai yin Ƙaho baya karya Azumi, wannan itace Magana mafi inganci – In sha Allah – kuma akan ta mafi yawancin Malamai suka tafi, kamar su Imam Malik da Imam Shafi’i kuma itace Fatawar Ibn Abbas da Ibn Umar da Ibn Mas’ud da Anas ɗan Malik da sauran su [Fathul Baariy 3/209].
Istimna’I [Menstruation]: shine fitar da Maniyyi.
A farko dai, bari mu tabbatar da haramcin wannan mummunar dabi’a musamman a cikin Watan Ramadana haka ma a cikin wani Watan da bashi ba, sai dai wadanda suka halastar da yin shi basu da wata hujja mai karfi akan wadanda suka haramta shi, saboda fadar Allah mabuwayi da daukaka inda yake cewa: ((su Muminai sune masu kiyaye farjojin su (5) basa bayyanar dasu sai ga ma’abota auren su ko abunda hannayen su suka mallaka na Bayi to anan su ba abun zargi bane (6) duk wanda ya nemi wata hanya daban wacce ba wannan ba to wadannan sune masu ketare iyaka (7)). [Suratul Muminoon]
Sai dai menene hukuncin Azumin wanda ya jarabtu da yin irin wannan mummunar dabi’a ta Haram?
Amsa: Azumin shi yayi, tare da haka kuma yana da zunubi saboda aikata Haramci da yayi, duk wanda yake neman fadada bincike kan wannan mas’alar, to ya duba littafin “Tamammul Minnah” na Shaykh Nasiruddenil Albaniy a shafi na 418.
Wanka saboda sanyaya jiki da Ruwa sakamakon ƙishi da zafin Rana.
Ƙarkashin haka an ruwaito cewa Annabi yana wayar gari ma da Janaba a jikin shi alhali yana Azumi sai yayi Wanka kamar yadda mukayi bayani a baya, kuma an ruwaito daga wani Sahabin Annabi (SAW): hakika naga Manzon Allah a wani waje ana zuba masa ruwa akai – alahli yana Azumi – saboda ƙishi da kuma zafin Rana [Abu Dawuda ya ruwaito]
@AnnasihaTv