MAGANIN CUTUTTUKAN DA SU KA SHAFI IDO


MAGANIN CUTUTTUKAN DASUKA SHAFI IDO. 

- Jan ido .
- kaikayin ido.
- zafin idon.
- kwantsa.
- zubar ruwa.
- ganin hayaki - hayaki.
 
 Duk mai fama da 'daya daga cikin wadannan cututtukannan zai iya amfani da daya daga cikin wadannan magunguna kamar haka:

1- Ahada garin si'itir da kwallin Ismud(Asmud) arinka sawa a ido safe da yamma kafin bacci. 

2- Asaka babban cokali biyu na furen albabunaj a ruwa rabin litre sai adorashi a wuta yayi minti goma sai abarshi ya huce atace a rinka wanke fuska dashi safe da yamma.

3- Arinka diga man albasa safe da yamma. 

4- Ahada kafra da ruwan zam - zam a dora a wuta idan kafran ya narke sai a rinka diga ruwan a ido duk bayan awa shida; yana wanke ido ya kara masa karfin gani.

TAMBIHI: Duk wanda baisan daya daga cikin wadannan magungunan ba, ko kuma ya sani amma bai fahimci yadda ake hadin ba; to muna bada shawarar kada yayi gaggawar amfani dashi har sai yaje wurin masu islamic chemist na gaskiya masu bada magani d siyar dashi abisa tsari na musulunci sai suyi mishi bayani, domin lafiya jarine baikamata ayi wasa da ita ba, ballantana kuma abunda yashafi lafiyar ido. 

Marasa lafiyarmu Allaah yabasu lafiya, wadanda ke dashi kuma Allaah yakara mana. 

Wallahu ta'ala A'alam.

Copied
Post a Comment (0)