AZUMIN MARA LAFIYA


AZUMIN MARA LAFIYA.

Rashin lafiya iri uku ne ga mai azumi:
1. Rashin lafiyan da ba zai cutar da mai azumi ba, kamar ƙujewa ko raunin da bai yi tsanani ba, ko ɗan zazzaɓi ko canjin yanayin jiki da makamantan cutaka masu sauki, ta yadda yin azumi ba zai cutar da lafiyar sa ba, ko ba zai haɓaka cutar ba, ko ba zai sa a samu jinkirin waraka ba. A wannan yanayi baya halatta mutum yasha azumi, dole yayi.
2. Rashin lafiyar da zai cutar da mutum in yayi azumi, ko zai haɓaka cutar ya ruruta ta, ko zai sabbaba jinkirin samun lafiya - musamman idan ba a yi amfani da magani akan kari ba, ko kuma a samu likita amintacce ƙwararre yace in mutum yayi azumi ko in ya daɗe bai ci abinci ba zai haifar masa da matsala ko zai kai ga salwantan ran sa. A wannan yanayi wajibi mutum yasha azumi har sai ya samu lafiya da karfi da kuzarin yin azumin.
3. Rashin lafiyar da idan anyi azumi ba za a galabaita ba, amma akwai ɗan wahala a ciki. A wannan yanayi ya halatta a sha azumi, kuma ya halatta a yi azumin, ma'ana idan yayi babu laifi, haka ma idan yasha shima babu laifi.

SANNAN RASHIN LAFIYA IRI BIYU NE:
1. Wanda ake tunanin warkewa daga cutar in sha Allaah: Mai irin wannan rashin lafiyar in ya sha azumi zai biya bayan ya samu lafiya.
2. Wanda ba a tunanin warkewa, bayan an kai maƙura wurin neman magani, ko kuma masana harkar lafiya ƙwararru amintattu sun ce babu maganin cutar sai dai a cigaba da dabarbaru ilã mã shã Allah (Duk da babu cutar da babu maganin ta, wanda ya sani ya sani, wanda ya jahilta ya jahilta -In ji Annabi s.a.w). To a wannan yanayi zai rinka ciyarwa ne (Kowane rana zai ciyar da miskini ɗaya rabin sã'i na irin abincin da aka fi ci a yankin su). Hukuncin sa zai zama kamar wanda ba zai iya azumi bane kwata-kwata.

✍🏻Rubutawa: Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
11/Ramadan/1441.
04/May/2020.

Kasance damu a tashar mu na Telegram@

Maza: https://telegram.me/almadeeniymodernschool

Mata: https://telegram.me/almadeeniymodernschoolfemale
Post a Comment (0)