KUNUN GERO MAI MADARA

*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*


*KUNUN GERO MAI MADARA*

KAYAN DA ZA KI TANADA
1. Madara
2. Gero
3. Sikari ko zuma
4. Fulawa ko cornflour

*YADDA ZA KI HADA KUNUN*

Ki sami gero ki wanke ki rege, sai ki kai a surfa miki, idan an sawo da shi daga surfe sai ki bakace ki cire dusar da ke ciki ki sake wankewa, ki baza shi a rana domin ya bushe. A gefe daya kuma sai ki dora tukunya akan wuta ki zuba madarar ruwa, idan kuma ta gari ki ke da ita sai ki kwaba ta tsararo ki dora akan wuta, idan ta tafaso sai ki debi wannan barzazzen geron ki zuba a cikin ruwan madarar da yake tafasa. 

Sai ki bar shi ya sake tafasowa, yadda idan kina shan kunun za ki iya tauna geron, ki rage wutar ki kwaba fulawa ko kuma cornflour da kauri, amma fa ba kauri kitibir ba sai ki ringa zubawa cikin ruwan madarar da gero domin ya daure ya yi kauri. Idan kaurin ya yi miki, sai ki kawo dakakken kaninfari dan kadan ki zuba a ciki, sai ki bar shi akan wuta na minti biyu zuwa biyu zuwa uku sannan ki sauke daga kan wuta. Ki zuba sikari ko zuma ki sha duminsa.


*✍Written by admins*
        *Sumayya &*
        *Fauziyya*

*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
      *WhatsApp Group*
      *0816 772 2658*
      *0803 466 1023*

Post a Comment (0)