ILLOLIN ZINA, LUWAƊI DA MAƊIGO 7

*07→ILLOLIN ZINA ,LUWADI DA MADIGO*


Magana ta farko: Za a kone shi da wuta, wannan shi ne fahimtar Sayyidina Abubakar da Aliyu da Ibnu Zubair da sauransu. (Duba Zadul Ma’ad da Adda’u waddawa’u da Sunan Al-kubra na Baihaki da sauransu).

• Magana ta biyu: Za a jefe shi da duwatsu har ya mutu, ya taba aure ko bai taba ba. Wannan ita ce fahimtar Sayyidina Umar da Abdullahi dan Abbas da sauransu. (Duba Raudatul Muhibbin na Ibnul kayyim).

• Magana ta uku: Za a samu ginin da ya fi kowane tsawo, a jefo shi daga can, sannan a biyo shi da duwatsu. An rawaito wannan magana daga Abubakar da Abdullahi dan Abbas. Sai ya zamo suna da fahimta biyu ke nan a mas’alar.

• Magana ta hudu: Za a jefo masa katanga. An rawaito wannan magana daga Aliyu bin Abu dalib.

• Magana ta biyar: Za a yi masa hukuncin mazinaci, idan yana da aure, ko ya taba yi sai a jefe shi, in kuma saurayi ne a yi masa bulala. Wannan ita ce fahimtar Abdullahi Ibnu Zubair.

Wadannan su ne maganganun sahabbai da almajiransu a kan hukuncin da za a yi wa mai luwadi. Babu ko shakka, idan muka dubi wadannan maganganu, za mu gane cewa yin luwadi ba karamin laifi ba ne a addinin Musulunci.


Zamu kwana a nan, a dakacemu 

Rubutawa:- Dr, Muhammad Rabi’u Umar Rijiyar Lemo, 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)