YADDA AKE SALLAR WUTIRI A TAƘAICE

YADDA AKE SALLAR WITRI A TAKAICE
Wasu na kiransa shafa'i da wutri, amma sunansa na sharia shine witri, dalilin da yasa wasu ke kiran shi *shafa'i da wutri* shine wani lokaci akan yi raka'a 2 kafin ayi wutrin. Amma sunan sa da sharia tasa masa shine wutri (ma'ana sallah mai mara) wanda ya kunshi duk nafilfilin da akeyi bayan Isha'i zuwa kafin fitowar Al-Fijr.

A takaice ga siffofi na wutri ko sallar dare da su ka tabbata a sunnah:
1. Raka'a 11.
2. Ko raka'a 9.
3. Ko raka'a 7.
4. Ko raka'a 5.
5. Ko raka'a 3.
6. Ko raka'a 1 gyal.

Anaso a rinka nau'antawa, idan yau an yi mai raka'a 3, gobe sai ayi mai 5, wataran ayi mai 11, wataran kaza... wataran ma za'a iya yin 1 gyal.

Raka'o'in za'a iya yin su bibiyu sai a cike da raka'a daya yazama mara(wato wutri), ko hudu-hudu sai a cike da 1 ko a cike da 3 yazama mara(wato wutri), ko kuma ayi hudun gabadaya ba tareda tahiya ba sai a karshe ayi tahiya a sallame.

Sannan za'a iya karanta duk abun da ya sawwaka na Qur'ani, amma a raka'o'i biyu (wadanda daga su sai raka'ar karshe) an fi so a karanta Suratul A'alaa (sabbih) da kuma Suratul Kaafiruun (Qulya), a raka'ar karshe kuma ana karanta Suratul Ikhlaas ne kadai (Qulhuwa).

Sannan wani lokaci an so a rinka yin Al-Qunut a raka'ar karshe na wutri, imma kafin ruku'u ko bayan dagowa daga ruku'u, sai mutum ya ďaga hannayen sa ya karanta lafazin Al-Qunut da ya tabbata a sunnah kamar haka:

اللهم اهدني فيمن هديت، وعافني فيمن عافيت، وتولني فيمن توليت، وبارك لي فيما أعطيت، وقني شر ما قضيت، فإنك تقضي ولا يقضى عليك، إنه لا يعز من عاديت، ولا يذل من واليت، تباركت ربنا وتعاليت، لا منجا منك إلا إليك.

Wani lokaci - bayan wannan addu'ar - anso a kara da salatin Annabi s.a.w tabbatacce kuma cikakke.

A karshe idan an sallame ba zikirorin da aka saba yi bayan sallar farilla akeyi ba, a'a akan karanta wannan addu'ar ce da ta zo a sunnah; sau uku:

سُبْحَانَ الْمَلِكِ الْقُدُّوسِ.

A na ukun sai a ďan ďaga murya sannan a cike da wannan👇🏻👇🏻

رَبِّ الْمَلَائِكَةِ وَالرُّوحِ

Allaah Yasa mudace.

Rubutawa: Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
20/11/2017

Post a Comment (0)