MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 21


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(21)

*ZAKKAR FIDDA KAI:*

 Allah (SWT) da rahamarsa,
ya tsara mana
(mu Musulmi) manyan ibadu guda biyu, su zama su ne kammaluwar wadan nan ibadu.

A nan ina nufin Azumin Ramalana da Aikin Hajji,
wadanda ya umarce mu da yin sallolin Idi a Karshen su, watau idin buda baki (Karamar Sallah) da Idin Layya (Babbar Sallah).

To babban abin da ya kamata hankalinmu ya jawu gare shi shi ne, bayan kamala kowane daya daga cikin wadan nan ibadu, sai Allah (SWT) ya umarce mu da mu ciyar da junanmu.

A Karshen Azumi sai ya tsara mana mu ciyar da junanmu abinci (Watau Zakkar Fidda-kai).

A Karshen aikin Hajji kuma, sai ya tsara mana mu ciyar da junanmu nama, (watau yanka Hadaya ko layya).

Abin nufi a nan shi ne, mu fahimci cewa ma’anar Ibadu a wannan addinin namu ita ce,
su koya mana hada kai (kamar yadda muka gani Kuru-Kuru a sallolin Idi Karama da babba) da taimakon juna

 (kamar yadda mu ka gani Kuru-Kuru a Zakkar fidda-kai da layya ko Hadya). 
Allah ya sa mu gane amin.

To yanzu sai mu shiga bayaninmu game da Zakkar fidda-kai.

Ma’anarta: Ita ce Zakkar da ake kira Zakkar buda-baki ko zakkar jukkuna.

 Domin a bambanta ta da Zakkar dukiya, wadda muke magana a kai.
Ita ce kuma har yau ake kira Zakkar kono.

Hukuncinta:
Zakkar fidda-kai ko zakkar kono, wajibi ce a kan kowane Musulmi, namiji da mace,
yaro da babba, "da ne ko bawa.
Me ake bayarwa?:

 Ana bayar da kwano guda, watau muddun Nabi hudu, a kowane mutum, daga abincin da mutanen gari suka fi amfani da shi. Mai gida ne yake fitar wa da iyalinsa wadanda yake ciyarwa, bayan ya fitar wa kansa.

Yaushe ake fitar da ita?:
Ana fitar da ita a rabar a safiyar sallah, kafin a tafi sallar Idi. Idan kuwa aka bari har sai bayan sallar Idi,
to ba Zakka sunanta ba. Ta koma daidai da kowace sadaka.

 Duk da cewa yana da kyau a bayar da ita tun kwana daya ko biyu kafin Idi. Domin Sahabban Annabi (SAW) haka suke yi.

*Su wa ake bai wa?:*

 Ana bayar da ita ne ga faKirai da miskinai,wadanda muka yi bayanin su a baya. Amma fa wannan ba ya na nufin idan kai faKiri ne ko miskini shi ke nan ba za ka fitar ba,
 a’a, lallai ne ka bayar ga wanda ya fi ka talauci.

Domin ba ta sauka daga kan mutum sai idan ya zama a safiyar Idi ba shi da abin da zai fitar bayan ya ciyar da iyalinsa.

*Ina za a kai?:*

Idan akwai wurin da hukuma ta ware, to yana da kyau a kai can. Amma lallai a kai a Kalla, kwana biyu kafin ranar Sallar.

Idan kuwa ba haka ba, to sai mutum ya raba wa faKiran da kansa. Babu laifi a ba wa limami ko malamin unguwa idan faKiri ne.

Ko za a iya bayar da Kima?:

Lallai ne a bayar da abinci. Sai idan babu abincin ko ba zai yi amfani ba.

*Hikimarta:* 
Babbar hikimarta, ita ce wadda muka ambata a baya. Watau ciyar da miskinai.
Hikima ta biyu kuma ita ce, cike kura-kuran da mai azumi ya yi da ladanta.

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)