*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*
*SEASONINGS AND SPICES //2*
*5. Curry:* Shi ma curry yana taka rawa wurin girki, especially in kina amfani da product din da ya dace, don wani gaskiya sai dai ya bata miki girki. Kuskure ne ace baki da wani curry da kike amfani dashi. Zaki iya amfani da Ducros yana da kyau gaskiya ko Tiger ni dai na yarda da biyun nan. Nasan akwai masu kyau da tsada da zaki nema don qawata abincin ki ba dole sai wainnan ba.
*6.Thyme:* Thyme amfanin sa a abinci bashi da yawa gaskiya, ina saka thyme a girki amma ba a ko ina ba, sannan shi kadan ake sakashi, wasu suna laftashi kaji shi har a bakin ka, to sai a yi kokari a rage.
*7. Onga:* A gaskiya kamfanin onga sun yi kokari da tun fitowar sa basu 'bata shi ba, onga yana taka rawa a girki, don in ban saka shi ba bana jin abincin ya kai mun. Onga akwai stew, wannan yana qara jan girki ne, ba zaki rinqa yin abinci fari sal ba kuma yana da dandano, sannan akwai classic da kuma chicken dama sauran su, dukkan su suna taka rawa sosai wurin gyara abinci.
*8. Madish:* Da ban san madish ba kuma bana amfani dashi amma shi ma na ga yana da sirri, musamman mai yajin shi, idan kika siye shi kin huta siyan garin yaji don sakawa a farfesu ko suya, akwai mai yaji akwai mara yaji shi ma yana gyara girki sosai.
*9. Benny:* Wasu suka ce mai kan zakara, a gaskiya ban wuce 5 month da fara amfani da benny ba, amma a gaskiya yana da mutuqar zaki wurin gyara taste din abinci, ki nema kasuwa kuma bashi tsada sosai.
*✍Written by admins*
*Sumayya &*
*Fauziyya*
*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
*WhatsApp Group*
*0816 772 2658*
*0803 466 1023*
